Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

NLC Ta Yi Watsi Da Ƙarin Kuɗin Man Fetur, Ta Ce Gwamnati Ta Saɓa Alƙawarin Da Aka Yi Da Ita

Kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC) ta ce ƙarin farashin fetur da aka yi kwanan nan abin firgici ne da tayar da hankali.

NLC ta kuma ce Gwamnatin Tarayya ta yi mata kafar ungulu bayan yarjejeniyar da suka cimma yayin tattaunawa kan mafi ƙarancin albashi, inda NLC ta amince da Naira 70,000 maimakon bukatarta ta Naira 250,000 saboda an tabbatar mata ba za a ƙara farashin fetur ba.

A wata sanarwa da Shugaban NLC, Kwamared Joe Ajaero, ya sanya wa hannu, kungiyar kwadagon ta bukaci a janye karin farashin man fetur da aka yi a fadin kasar.

Sanarwar mai taken, “Mun Ji An Yaudare Mu,” ta ce: “Muna cike da jin cewar an ci amanarmu, ganin yadda gwamnatin tarayya ta ƙara farashin fetur a ɓoye. Daya daga cikin dalilan da yasa muka amince da Naira 70,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi shi ne fahimtar cewa ba za a ƙara farashin fetur ba, duk da cewa mun san cewa Naira 70,000 ba zai wadatar ba.

“Muna sane sosai lokacin da Shugaban Kasa ya ba mu zaɓi mai wuya tsakanin Naira 250,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi (wanda zai sa farashin fetur ya tashi zuwa tsakanin Naira 1,500 zuwa Naira 2,000) da kuma Naira 70,000 (farashin ya tsaya yanda yake), muka zaɓi na biyun saboda ba za mu iya amincewa da ci gaba da wahalar da ƴan Najeriya ba.

“Amma ga shi, kasa da wata daya bayan haka, gwamnatin ma ba ta fara biyan sabon albashin ba, sai ga wani al’amari da ba za mu iya bayyanin yanda ya samo asali ba.”

“Wannan abu ne mai rikitarwa kuma kamar a mafarki mai firgirtarwa”.