Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

NNPCL: NLC Ta Kira Zaman Gaggawa Kan Ƙarin Farashin Fetur

Ƙungiyar Ƙwadago ta Najeriya, NLC, ta bayyana shirinta na yin zaman gaggawa dangane da karin kashi 45 cikin 100 a farashin man fetur da Kamfanin Man Fetur na Najeriya, NNPCL, ya yi kwanan nan.

Wannan na zuwa ne yayin da ƙungiyar ta buƙaci Kamfanin Man Fetur na Najeriya (NNPCL) da ya janye ƙarin farashin da ya kai Naira 855 zuwa Naira 897 da ya yi a ranar Talata.

Ƙungiyar Ƙwadago ta Najeriya ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar, Joe Ajaero, ya sanya wa hannu a ranar Talata, a matsayin martani ga ƙarin farashin fetur ɗin.

NLC ta kara da cewa gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu ta ci amanar ta.

Haka kuma, ƙungiyar ta bukaci a saki duk masu zanga-zangar da ake tsare da su, sannan kuma ta nemi a janye ƙarin farashin wutar lantarki da aka yi a watan Afrilu na 2024 da ya kai kashi 250 cikin 100.