Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

NOA Ta Yabawa Davido Bisa Tallata Najeriya a Duniya, Ta Ce Ya Zama Wakilin Ƙasa Na Gari

Hukumar Wayar da Kan Jama’a ta Ƙasa (National Orientation Agency), ta yabawa fitaccen mawaƙi David Adedeji Adeleke wanda aka fi sani da Davido, bisa yanda ya wakilci Najeriya cikin nuna ƙwazo a wata tattaunawa da aka yi da shi a tashar talabijin ta CKO a ƙasar Faransa.

A cewar Darakta Janar na NOA, Mallam Lanre Issa-Onilu, “Mun karɓi saƙon da ya zo daga tattaunawarka inda ka jaddada cewa ba Najeriya kadai ba, duk inda ka je akwai haɗari, ciki har da Paris da Atlanta.”

Ya ce irin wannan kalami na nuna gaskiya da ƙwarewa, yana taimakawa wajen ruguza tunanin da ake da shi na cewa Najeriya cike take da matsaloli fiye da sauran ƙasashe.

Issa-Onilu ya ce saƙonka ya yi daidai da sabon tsarin “National Identity Project” na hukumar wanda ke ƙoƙarin kafa sahihin salon yanda za a riƙa kallon ƴan Najeriya a duniya da kuma a gida.

KARANTA WANNAN MA: Gwamnati Ta Caccaki Sarkin Mota Bayan Ya Soki Ma’aikatan Gwamnati A Tallen Motarsa

Hukumar ta bayyana cewa irin wannan tsayawa kan gaskiya da nuna kishin ƙasa zai ƙarfafa tunanin ƙasa mai albarka duk da ƙalubalen da ake fuskanta.

“Mun gamsu da irin wannan salo na yaɗa kyakkyawar ɗabi’ar ƙasa da gaskiya cikin natsuwa,” in ji shi.

NOA ta buƙaci Davido da ya ci gaba da nuna halin kirki da ƙwarewa wajen wakiltar Najeriya a dandalin duniya, yana mai cewa hakan zai ƙara farfaɗo da martabar ƙasa.

Har ila yau, ya jaddada cewa irin wannan wakilci daga fitattun ƴan ƙasa na buƙatar yabo da goyon baya daga gwamnati da al’umma.

A ƙarshe, NOA ta bayyana fatan cigaba da haɗin gwiwa da Davido wajen tallata al’adun Najeriya da abubuwan alheri da take da su a fagen nishaɗi da al’umma baki ɗaya.