Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

PDP Na Tattaunawa Da Kwankwaso Da Peter Obi Kan Zaɓen 2027 — Kakakin Jam’iyyar

Jam’iyyar PDP ta fara tattaunawa da tsohon gwamnan Jihar Kano, Rabiu Kwankwaso da kuma dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party (LP) a zaben 2023, Mista Peter Obi, kan zaben 2027 mai zuwa.

Mataimakin Kakakin Jam’iyyar PDP na Kasa, Ibrahim Abdullahi ne ya bayyana hakan a wata hira da aka yi da shi a tashar Channels Television a yau Litinin.

Abdullahi, kamar yanda mafi yawan mambobin jam’iyyar suke faɗa, ya danganta faduwar PDP a zaben 2023 da ficewar Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso daga jam’iyyar zuwa wasu jam’iyyu, watanni kaɗan kafin zaben shugaban kasa, tare da wasu dalilai.

Duk da haka, ya nuna kwarin guiwa cewa matakan da jam’iyyar ke dauka wajen jawo wadannan fitattun ‘yan siyasa da suka taba kasancewa cikin iyalin PDP zai haifar da sakamakon da ake so kafin zaɓen 2027.

Abdullahi ya ce, “Mun rasa Kwankwaso, mun rasa Peter Obi — duk wadannan mutanen — muna tunanin inda suna cikin jam’iyyar, da mun lashe zaben,” in ji shi.

“APC ta fi mu ne da sama da (kuri’u) miliyan daya daga cikin wadannan sunaye da na ambata da ɗaya daga cikinsu zai rufe wannan gibin da kuma yanzu muna kan mulki, kuma da tabbas ‘yan Najeriya ba za su fuskanci wannan bakin ciki da damuwar ba a kasa.”

Ya jaddada cewa, domin samun cikakkiyar nasara, ana cigaba da tattaunawa don dawo da Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar LP da Rabiu Musa Kwankwaso dan takarar jam’iyyar NNPP a zaben 2023, zuwa jam’iyyar PDP kafin zaben 2027.