Jam’iyyar PDP ta fara ƙoƙarin sake gyara tsarinta domin fuskantar babban zaɓen 2027, inda jiga-jigan jam’iyyar suka tabbatar da ci gaba da tattaunawa da Peter Obi na jam’iyyar Labour Party da sauran tsoffin ƴan jam’iyyar da suka fice.
A wata hira da aka yi da tsohon Ministan Yaɗa Labarai Jerry Gana a shirinsa na Focus Nigeria da gidan talabijin na AIT ke watsawa, ya bayyana cewa PDP na tuntuɓar fitattun ƴan siyasa daga Kudu, musamman ganin yadda ake ƙoƙarin maida tikitin shugaban ƙasa na 2027 zuwa yankin.
“Eh, me ya sa ba za mu tuntuɓe shi ba? Ai namu ne,” in ji Jerry Gana, yana mai cewa da shi ne tsohon mataimakin shugaban ƙasa “da na ce masa a 2023: Peter, kai ne mataimakinmu a 2019, yanzu zamu mara maka baya.”
Sai dai ya ƙara da cewa har yanzu ba a fara tattaunawa kai tsaye da Obi ba, amma ana ci gaba da ganawa da wasu mutane masu kusanci da shi.
“Na haɗu da shi, kuma na yi sa’o’i ina magana da waɗanda ya yarda da su. A hankali muke tafiya,” in ji Gana.
WANI LABARIN: Batun Sai Ɗalibai Sun Kai Shekaru 12 Zasu Shiga Ƙaramar Sikandire Ba Shi Da Tushe – Ma’aikatar Ilimi
A cewar Ibrahim Abdullahi, mataimakin mai magana da yawun PDP na ƙasa, “Peter Obi babban jari ne ga kowace jam’iyya. A gaskiya, namu ne, kuma muna so mu dawo da shi.”
Obi ya fice daga PDP ne a watan Mayun 2022 kafin zaɓen fidda gwanin shugaban ƙasa, yana mai bayyana cewa jam’iyyar ta rasa tafarkin da ke ba da dama ga “bayar da gudunmawa mai ma’ana.”
A halin da ake ciki, PDP na kuma fuskantar barazanar rushewa daga cikin gida, inda tsohon gwamnan Jihar Ekiti, Ayodele Fayose, ya bayyana cewa “jam’iyyar na iya zama ta huɗu a babban zaɓe mai zuwa.”
A cewarsa, “Ruhin PDP ya tafi, rai ya fita, jiki ne kawai ya rage.”
Cikin wani abin mamaki kuma, tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar ya fice daga PDP, yana mai cewa jam’iyyar ta yi hannun riga da ainihin ƙa’idojin da aka kafa ta da su tun 1998.