Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

PDP Ta Yi Allawadai Da Jawabin Tinubu Kan Halin Da Ƙasa Ke Ciki

Jam’iyyar Peoples Democratic, PDP, ta bayyana jawabin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu kan Halin da Ƙasa ke Ciki na ranar Litinin a matsayin wani baƙin labari da yake tunawa ƴan Najeriya irin a alƙawuran Muhammadu Buhari waɗanda ba su tsinana komai ba.

PDP ta ƙara da cewa, jawabin ya ƙara sare guiwa ga har magoya bayan gwamnatin, waɗanda da dama daga cikinsu ke shan baƙar wahala ta matsanancin halin rayuwar da janye tallafin man fetur ya jawo.

Da yake jawabi ga manema labarai a yau Talata, Sakataren Yaɗa Labarai na jam’iyyar, Debo Ologunagba ya ce, alƙawuran Tinubu kawai sha-ci-faɗi ne, inda ya ƙarfafa cewar kula da yanayin janye tallafi abu ne da ya fi ƙarfin wannan gwamnatin.

Ya ce, jawabin Tinubun ya nuna irin rashin sanin makamar da APC ke ciki, inda ya ce, ya kamata su sani cewa, ƴan Najeriya ba su taɓa ƙwalawa irin wannan ba.

Sakataren Yaɗa Labaran na PDP, ya kuma ce, inda an iya yin abun da ya dace da ba za a siyar da man fetur sama da naira 150 a Najeriya.