Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Rainin Hakali Ne Ke Sa Gwamnati Shirin Ƙarawa Shugabannin Siyasa Albashi – ADC

Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ta yi watsi da shirin RMAFC na ƙara wa manyan masu riƙe da muƙaman siyasa albashi, tana kiran matakin “kurakurai ne na marasa tausayin talakawa.”

A cewar mai magana da yawun jam’iyyar, Mallam Bolaji Abdullahi, “a lokacin da ake fama da hauhawar farashin kaya, tsadar mai da kuma mafi ƙarancin albashi da ba a biya a wasu wuraren, ƙarin albashi ga ƴan siyasa rainin hankali ne.”

Ya ce ko da shugaban RMAFC ya kira tsohon tsarin “ba ya isarwa, ba shi da inganci kuma ya tsufa,” ADC ta jaddada cewa “wannan albashin na yanzu ana tura su da alawus-alawus masu nauyi da ba a bayyanawa,” abin da ke haifar da rayuwar alatu ga shugabannin.

Jam’iyyar ta tunasar da cewa “mafi ƙarancin albashi naira 70,000 ne, amma hauhawar farashi ta cinye darajarsa, kuma ma’aikata ba sa samun alawus-alawus irin na manyan gwamnati.”

“A dakatar da wannan shiri nan take,” in ji ADC, “a maida hankali kan ɗaga albashin ma’aikata, biyan su a kan lokaci da ƙarfafa tallafin jin kai ga masu rauni.”

Jam’iyyar ta ce “gwamnati ba ta da haƙƙin neman ƙarin sadaukarwa daga talaka yayin da take sauƙaƙa rayuwar kanta kaɗai.”

ADC ta yi gargaɗin cewa za ta ci gaba da matsa lamba a majalisa da kotu idan ya zama dole, domin “a bai wa talaka fifiko maimakon cika aljihun manyan masu mulki.”