Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

RASHIN WUTA: An Gano Matsalar Layin Wuta A Ugwuaji-Apir, Za A Fara Gyara A Yau

Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Najeriya (TCN) ya gano matsalar da ta jawo katsewar wuta a layin wutar lantarki na Ugwuaji-Apir 330kV Double Circuit.

An gano matsalar a Igumale na Jihar Benue, ta hannun tawagar ma’aikatan TCN da misalin karfe 5 na yammacin Laraba, 23 ga watan Oktoba, 2024.

Matsalar ta samo asali ne daga layin wutar da ya karye a wani bangare na dajin mai duhun bishiyoyi a yankin.

TCN ta fara shirye-shiryen jigilar kayan aiki da na’urori zuwa wurin domin fara aikin gyaran.

Saboda yanayin yankin da ke da wahala, manyan motocin aiki, ciki har da bulldozer da Hiab za a tura daga ofishin TCN na yankin Enugu don tabbatar da daidaita layin wutar.

Layin wutar Ugwuaji-Apir mai tsawon kilomita 215 ya samu matsala a ranar Litinin, 21 ga Oktoba, 2024, wanda ya haddasa katsewar wuta a fadin yankin Arewa maso Gabas, Arewa maso Yamma, da wasu sassan Arewa ta Tsakiya.

Yunkurin da aka yi a baya na gano matsalar bai yi nasara ba sai a jiya.

TCN ta tabbatar wa jama’a cewa za a fara aikin gyaran nan take, tare da godiya ga gwamnatoci da kuma masu amfani da wuta a jihohin da abin ya shafa saboda hakurin da suka nuna a lokacin wannan matsalar.