Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Rikici Ya Ɓarke A Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Yamma Kan Tallafin Karatu

A wani rikici da ke ci gaba da girmama, hukumar North West Development Commission (NWDC) ta shiga cece-kuce a cikin gida dangane da wani sabon shirin bayar da tallafin karatu zuwa ƙasashen waje ga matasa daga yankin Arewa maso Yamma, inda wasu daga cikin mambobin kwamitin hukumar suka musanta cewa an tattauna batun a wani zama, duk da cewa shugabancin hukumar ya ce an sanar da shugaban kwamitin ta cikin wata takarda kamar yadda dokar kafa hukumar ta tanada, kamar yadda DAILY TRUST ta rawaito.

A cewar wani mamba na kwamitin da ya buƙaci a sakaya sunansa, “ba a taɓa yin magana ko tattauna wannan shiri a kowanne zama na kwamitin ba,” yana mai zargin cewa wasu mutane daga wajen hukumar ne suka yi katsalandan wajen wallafa sanarwar da kuma tsara shirin ba tare da bin ƙa’ida ba.

Sai dai Daraktan Hukumar, Farfesa Shehu Abdullahi Ma’aji, ya ce “mun tura takardar sanarwa ga shugaban kwamitin a ranar 28 ga Afrilu, 2025, don sanar da niyyarmu ta ƙaddamar da shirin tallafin karatu ga matasan jihohin Arewa maso Yamma guda bakwai,” yana mai cewa manufar ita ce bai wa matasa damar samun ilimi a ƙasashen waje domin su dawo su taimaka wajen bunƙasa yankinsu.

WANI LABARIN: Gwamnatin Tarayya Za Tai Ayyukan Hanyoyi Na Sama Da Naira Tiriliyan 1.8 A Jihohi 12

Shi kuma shugaban kwamitin, Lawal Sama’ila Abdullahi, ya ce “sanarwar da aka fitar ba ta da tushe balle makama, saboda ba mu taɓa tattaunawa akanta ba,” yana mai cewa “na kira zama na gaggawa da za a yi ranar Alhamis don duba lamarin.”

Farfesa Ma’aji ya dage cewa hukumar ba ta karya wata doka ba, domin “abin da muka fara kawai shi ne neman tantance waɗanda za su cancanta, ba mu aika kowa zuwa ƙasashen waje ba tukuna,” yana mai cewa wasu mutane ne ke “nuna ƙin jinin shirin saboda zai fi amfanar ƴaƴan talakawa.”

Ya ƙara da cewa shirin zai kasance na haɗaka da wasu ƙasashen da za su ɗauki nauyin kuɗin karatu gaba ɗaya ko rabi, sannan hukumar za ta cika sauran, yana mai cewa “za mu yi amfani da wannan dama don ceto yankinmu daga koma-bayan da yake ciki a fannin ilimi.”