Wani rikicin sarauta a yankin Maraba Udege, karamar hukumar Nasarawa, ya haddasa mutuwar wata uwa da ɗanta, tare da raba mutane da gidajensu.
Bayanai sun nuna cewa rikicin ya barke ne tsakanin ƙabilun Afo daga unguwannin Angwan Dutse da Angwan Kasa, sakamakon takaddama kan mallakar fili.
Baya ga rasa rayuka, an kona gidaje da dama yayin fadan.
A ranar Laraba, Gwamnan Jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya kai ziyara yankin da abin ya shafa domin tantance halin da ake ciki.
“A matsayinmu na gwamnati, za mu yanke hukunci kan zaman lafiya a kasa. Ba za mu bar abubuwa su cigaba da kasancewa yanda suke ba,” in ji Gwamna Sule yayin ganawa da jama’a.
Gwamnan ya ce bincike ya tabbatar da mutuwar mace da ɗanta, amma ana ci gaba da tantance adadin mutanen da suka rasa rayukansu.
Gwamnan ya sanar da cewa gwamnatin jiha za ta naɗa wani jami’i da zai kula da yankin Maraba Udege domin samar da mafita kan rikicin.
Sule ya bukaci al’ummar yankin su zauna lafiya, domin cigaban yankin, musamman ma da ake fatan cigaba da ayyukan hakar ma’adanai a yankin na Udege.