Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Rikicin Manoma Da Makiyaya Ya Jawo Mutuwar Mutane Da Dama A Kwande, Jihar Benue

Mutane da dama sun rasa rayukansu a kauyukan Karamar Hukumar Kwande da ke Jihar Benue bayan wadanda ake zargin makiyaya ne sun kai hari a yankunan.

Wani shaida ya ce, har kawo yanzu akwai mutane da dama da suka bace, wasu da raunukan harbin bindiga a jikinsu yayinda aka kone gidaje da dama.

Wani mazaunin yankin ya ce, hare-haren sun fara ne kimanin mako guda da ya gabata, yayinda yai kamari a karshen makon da ya wuce inda ya kai zuwa kauyukan Moon, Mbaikyor, Mbadura da kuma Ilyav.

WANI LABARIN: Gobara Ta Lakume Dukiya Mai Yawa A Kauyukan Jigawa

A nata bangaren, kungiyar makiyaya ta Miyetti Allah Cattle Breeders Association (MACBAN) ta ce, an samu rikici tsakanin makiyaya da wasu ‘yansintiri a yankin bayan an kwacewa makiyayan dabbobinsu.

Kungiyar ta ce, an kashe makiyaya a yayin rikicin, sai dai kawo yanzu an fara samun zaman lafiya a sanadiyyar shiga tsakanin da shugabancin sojoji da sauran jami’an tsaro suka yi a jihar.

Lokacin da aka tuntubi Jami’in Hulda da Jama’a na Operation Whirl Stroke (OPWS), Flight Lieutenant DO Oquah, ya ce an magance matsalar, yayinda ya bayyana cewa bai san adadin mutanen da suka rasa ransu a dalilin rikicin ba.