Jigo a Jam’iyyar PDP, Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Sule Lamido, ya nemi a kori Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, da tsoffin gwamnonin jihohin Benue da Abia, Samuel Ortom da Okezie Ikpeazu, daga jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) saboda zargin yin aiki da gangan don cutar da jam’iyyar a zaɓen 2023.
Yayin da ake tattaunawa da shi a shirin Politics Today na Channels Television, Lamido ya zargi shugabancin jam’iyyar da jinkirin ɗaukar mataki kan “rashin ladabi” da ya ce ya daɗe yana faruwa, yana mai cewa: “Dukkan waɗannan ƴan jam’iyya… waɗanda suka yi kamfen a kan a ƙi PDP a zaben 2023, kuma suke cewa za su yi aiki don nasarar APC a 2027, ya zama wajibi a kore su daga jam’iyyar.”
- JIGAWA: Garko Ta Haɗejia Na Cikin Damuwa, Ɗaruruwan Almajirai Da Iyalai Sun Rasa Matsugunnai Sakamakon Mamakon Ruwan Sama
- KATSINA: Aƙalla Mutane 50 Ne Suka Mutu a Hare-Haren Malumfashi
- BORNO: Ƴan Boko Haram Sun Kashe Jami’an Tsaro Sun Yi Garkuwa Da Wasu A Konduga
- Sanata Wadada Ya Bayyana Ficewa Daga SDP Saboda Rikicin Da Ya Ƙi Ci Ya Ƙi Cinyewa
- TATTALIN ARZIƘI: Ajiyar Kuɗin Waje ‘Foreign Reserve’ Na Najeriya Ya Kai Dala Biliyan 41 – Fadar Shugaban Ƙasa
Ya bayyana cewa rikicin ya samo asali ne tun bayan taron fidda gwani na 2022, inda wasu suka fusata suka juya wa jam’iyyar baya.
“Tun daga wancan lokaci mutane sun fice daga jam’iyya suka kuma yi mata adawa,” in ji shi, yana ƙari da cewa dokar PDP ta bayyana hukunci ga masu karya ƙa’idar jam’iyya.
Lamido ya kuma sanar da dakatar da halartarsa taron kwamitin amintattu (BOT) na jam’iyyar har sai an hukunta waɗanda suka aikata laifin.
A rana guda, kwamitin zartarwa na PDP (NWC) ya fitar da gargaɗi ga dukkan mambobin da ke nuna goyon baya ga Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027, yana kiran hakan “barazana ga zaman lafiya da ɗorewar jam’iyya.”
Kakakin jam’iyyar, Debo Ologunagba, ya ce: “Zamu yi tsattsauran hukunci” idan ba a daina irin wannan ba, yana kuma nanata muhimmancin kare makomar jam’iyyar domin zaɓe mai zuwa.
An shirya babban taron ƙasa na PDP a ranar 15 da 16 ga Nuwamba a Ibadan, Jihar Oyo, wanda ka iya zama matakin da zai tantance makomar jam’iyyar.