Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

RIKICIN SARAUTA: Sarki Sunusi Da Sarki Aminu Sun Naɗa Galidiman Kano Daban-Daban

Masarautar Kano ta shiga wani sabon yanayi na ban mamaki bayan da Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero, da Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, suka naɗa mutane biyu daban-daban a matsayin Galadiman Kano a rana ɗaya.

Aminu Ado Bayero ya naɗa ɗan uwansa, Alhaji Sanusi Lamido Ado Bayero, a matsayin sabon Galadiman Kano a fadar Nassarawa, yayin da Muhammadu Sanusi II ya naɗa Alhaji Munir Sanusi Bayero, Hakimin Bichi, a matsayin Galadiman Kano a babbar fadar Kano.

A babbar fadar, Sarki Muhammadu Sanusi II ya kuma naɗa wasu manyan masu riƙe da sarautun gargajiya guda huɗu don su riƙe wasu muhimman muƙamai a masarautar.

KARANTA WANNAN: Gwamna Abba Kabir Zai Samu Goyon Bayan Ma’aikatan Jihar Domin Yin Tazarce

Ya shawarci sabbin masu riƙe da muƙaman sarautar da su kasance abin koyi wajen nuna biyayya, tawali’u da kuma kulawa da talakawa.

“An zaɓe ku bisa tarihin aikinku da na iyalanku; yawancin ku kun nuna biyayya da kishin masarauta, iyali da kuma jihar baki daya,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa, “Mun san irin ayyukan da kuke yi tuntuni, kuna taimakawa mabuƙata da kuma bada gudunmawa ga ci gaban al’umma. Ina roƙonku da ku ci gaba da irin wannan, da ku duba tarihi da kuma halayen iyayenku. Allah Ya taimaka muku wajen sauƙe wannan nauyi da aka dora muku,” in ji Sarki Sunusi.