Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Sai Ranar 15 Ga Satumba Man Ɗangote Zai Shiga Gidajen Man Najeriya – NNPC

Matatar Man Fetur ta Dangote zata fara cika kasuwar man fetur da mai daga ranar 15 ga Satumba, 2024, kamar yanda Kamfanin Man Fetur na Najeriya, NNPCL, ya sanar. 

Sanarwar da Olufemi Soneye, Jami’in Hulda da Jama’a na NNPCL ya fitar a jiya Alhamis, ta tabbatar da cewa farashin fetur zai kasance karkashin gwargwadon yanayin yanda kasuwa ta nuna.

Matakin ya biyo bayan fara tace man fetur da Matatar Dangote ta yi a makon da ya gabata.

Mista Adedapo Segun, Mataimakin Shugaban Sashen Man Fetur na NNPC Ltd, ya bayyana cewa an riga an soke tsarin kayyade farashin man fetur a harkar kasuwancinsa, inda yanzu kasuwa ce ke da iko a kan farashin.

Akwai jita-jita da ke cewa NNPCL na da hannu a cikin ƙayyade farashin man, amma wannan ƙarin bayani ya kawo ƙarshen wannan raɗe-raɗin.

NNPCL ya kuma ƙara bayyana cewa rashin isasshen kuɗin ƙasashen waje yana taka rawa wajen haifar da sauyin farashin man fetur, wanda yanzu ke ƙarƙashin ikon kasuwa, bisa tanadin dokar albarkatun mai ta PIA.

A lokacin da yake jawabi kan fara jigilar fetur daga Matatar ta Dangote, Segun ya ce suna jiran ranar 15 ga Satumba da aka tsara don fara jigilar man, sannan ya tabbatar da cewa matsalar karancin man fetur za ta ragu nan da yan kwanaki masu zuwa.