Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

SAKAMAKON ZAƁEN CIKE GURBI: Yanda Ta Kaya Tsakanin APC, PDP, APGA Da NNPP A Zaɓukan Da Aka Gudanar Ranar Asabar

Daga: Kabiru Zubairu Birnin Kudu

Zaɓukan cike gurbi da aka gudanar a ranar Asabar sun haifar da manyan sauye-sauye a fagen siyasar Najeriya, inda jam’iyyun PDP, APC, APGA da NNPP suka yi takara a jihohin ƙasar, kuma sakamakon ya bayyana irin karɓuwar kowacce jam’iyya a yankunanta.

A Oyo, ɗan takarar PDP, Folajimi Oyekunle, ya lashe kujerar majalisar wakilai ta Ibadan North da ƙuri’u 18,404, inda ya doke abokin hamayyarsa na APC, Adewale Olatunji, wanda ya samu kuri’u 8,312.

INEC ta sanar da nasarar nasa a cibiyar tattara sakamako ta Ikolaba High School, inda mai bayyana sakamakon zaɓen, Abiodun Oluwadare, ya ce: “Oyekunle na PDP, bayan cika dukkan ƙa’idojin doka, ya zama wanda ya lashe zaɓen.”

Wannan nasara ta biyo bayan rasuwar tsohon mai riƙe da kujerar, Olaide Akinremi na APC, wanda ya rasu a watan Yuli.

A Kaduna, APC ta ƙwace Chikun/Kajuru karo na farko tun shekarar 1999 da ƙuri’u 34,580 ga Felix Bagudu, tare da nasara a Zaria Kewaye da Basawa inda Isa Haruna Ihamo da sauran ya lallasa abokan takara.

Jigawa ma ba a bar ta a baya ba, inda Mukhtar Rabi’u Garki na APC ya samu kuri’u 38,449 ya kayar da PDP da NNPP a Babura/Garki, yayin da a Adamawa, Misa Musa na APC ya lashe kujerar Ganye da bambancin ƴan ƙuri’u 129.

Anambra ta ga sabon tashin APGA, inda Emmanuel Nwachukwu ya samu ƙuri’u 90,408 ya doke APC a zaɓen majalisar dattijai na Anambra South da aka gudanar sakamakon rasuwar Sanata Ifeanyi Ubah a 2024.

Haka nan, Adesola Ayoola-Elegbeji ta APC ta yi nasara a Remo, Ogun, da ƙuri’u 41,237, yayin da Hassan Shado ya yi fice da nasara a Okura, Kogi da ƙuri’u 55,073 duk da ƙarancin masu kaɗa kuri’a.

A Edo, APC ta ci gaba da tabbatar da ikonta inda Omosede Igbinedion ta doke PDP a Ovia da ƙuri’u 77,053, sannan Joseph Ikpea ya lashe kujerar Sanata na Edo Central da rinjayen ƙuri’u 105,129.

Anambra ta sake haskakawa da nasarar APGA a Onitsha North 1, inda Ifeoma Azikiwe ta kayar da sauran ƴan takara da ƙuri’u 7,774, a yayin da NNPP ta ɗaga murya a Kano ta hanyar cin nasara a Bagwai/Shanono inda Dr Ali Kiyawa ya samu ƙuri’u 16,198, duk da cewa APC ta lashe sabon zaɓen a Ghari/Tsanyawa da ƙuri’u 31,472.

Waɗannan sakamako sun nuna irin karonbattar siyasa da ke gudana, da yadda jam’iyyun ke raba rinjaye bisa ƙarfi da kuma amincewar jama’a a sassa daban-daban na ƙasar.