Babban Sakataren Hukumar Kula da Ilimi Matakin Farko, UBEC, Hamid Bobboyi ya bayyana cewar, sama da kaso 30 cikin 100 na malaman makaranta da ke koyarwa a makarantun Najeriya sun ajjiye cikin shekaru uku da suka gabata.
Bobboyi ya bayyana hakan ne a wajen bayar da horo na kwanaki shida wanda Hukumar Kula da Ilimi Matakin Farko ta Jihar Kano, haɗin guiwa da UBEC suka shirya a ranar Alhamis.
Ya bayyana yanayin rasa malaman a matsayin abin tsoratarwa, inda ya ce wasu malaman sun yi ritaya, yayin da wasu kuma suka ajjiye aiki domin neman aikin da ya fi daraja ba tare da an cike gurabensu ba.
Shugaban na UBEC ya kuma yabawa Gwamnatin Jihar Kano bisa ƙoƙarin ɗaukar matakan kare matsalar ƙarancin malamai ta hanyar ɗaukar sabbin malamai da cike guraben waɗanda suka yi ritaya, inda kuma yai kira ga sauran jihohi da su yi koyi da hakan.
Ya kuma jaddada buƙatar samar da walwala ga malamai, waɗanda ya ce suna da matuƙar muhimmanci wajen samar da ingantattun shugabannin gobe.