Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Sanata Natasha Ta Ce Ba Za Ta Ƙyale Hukuncin Da Majalissar Dattawa Tai Ma Ta Ba, Za Ta Ɗau Mataki

Sanata mai wakiltar yankin Kogi ta Tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan, ta ce za ta ƙalubalanci hukuncin dakatar da ita na tsawon wata shida a gaban kotu, bayan saɓanin da ta samu da Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, kan wurin zama a zauren majalisar.

Lauyan sanatar, Victor Giwa, ya ce matakin da majalisar ta ɗauka ya saɓa wa umarnin kotu.

Giwa ya bayyana haka ne a tattaunawarsa da jaridar The PUNCH, bayan da majalisar ta dakatar da Akpoti-Uduaghan tare da korar ta daga harabar majalisar dokoki ta ƙasa.

Haka kuma, Ƙungiyar Lauyoyi ta Najeriya (NBA) da jam’iyyun adawa sun soki matakin majalisar, inda suka ce ba ta bai wa sanatar isasshen lokaci don gabatar da ƙarar da ta shigar na zargin cin zarafinta da ta yi wa Akpabio ba.

Lauyan ya bayyana cewa, “Dakatarwar da aka yi wa Sanata Natasha ba ta da inganci, domin akwai umarnin kotu da ke hana Majalisar Dattawa ɗaukar mataki a kan lamarin har sai an yanke hukunci a kotu.”

Giwa ya ƙara da cewa, idan har Akpoti-Uduaghan ba ta ɗauki matakin shari’a ba, dakatarwar na iya ci gaba da aiki.

Ya kuma bayyana cewa kotu za ta hukunta waɗanda suka saɓa wa umarnin shari’a.

“Kotu ta bayar da umarni a dakatar da duk wani mataki na ladabtarwa, amma duk da haka, majalisar ta saɓa wa wannan umarni. Mun dawo kotu, kuma za mu sanar da ita cewa sun aikata hakan ne duk da an sanar da su, har da Shugaban Majalisar Dattawa,” in ji Giwa.

A yayin zaman majalisar, Kwamitin Ladabtarwa na Majalisar ya zargi Akpoti-Uduaghan da saɓa dokokin majalisa, inda ya bada shawarar dakatar da ita.

Majalisar ta amince da shawarwarin kwamitin, inda ta yanke hukuncin dakatar da ita daga dukkan harkokin majalisa daga ranar 6 ga watan Maris, 2025.

Dakatarwar ta haɗa da rufe ofishinta, janye tsaronta, da dakatar da albashinta, amma an bar albashin hadimanta su ci gaba da zuwa hannunsu.

Sanatar ta yi Allah-wadai da hukuncin tare da cewa, “Ba za a ci gaba da wannan zalunci a kaina ba. Zan ɗauki matakin da ya dace.”

A halin da ake ciki, NBA da wasu fitattun ƴan siyasa irin su Atiku Abubakar da Peter Obi sun yi Allah-wadai da hukuncin, inda suka ce an yi wa sanatar rashin adalci.

Ƙungiyar Lauyoyi Mata ta NBA ta buƙaci a tabbatar da adalci, tana mai cewa dakatarwar wata hanya ce ta murƙushe ƴancin sanatar.

Har yanzu dai lamarin na ci gaba da jawo cece-kuce, yayin da ɓangarori daban-daban ke faɗin albarkacin bakinsu kan lamarin.