Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Sanatoci Na Shirin Yin Dokar Da Za Ta Tilasta Tura Sakamakon Zaɓe Ta Na’ura

Majalissar Sanatocin Najeriya ta shirya yin gyaran dokar zaɓe domin bai wa ƴan Najeriya mazauna ƙasashen waje damar yin zaɓen shugaban ƙasa da kuma tilasta wa Hukumar Zaɓe tura sakamakon zaɓe ta na’ura.

Majalissar ta bayyana hakan ne a wajen taron da ta shirya a Ikot Ikpene ta Jihar Akwa-Ibom, inda ta ƙara da cewar, ta shirya yin dokar kafin zaɓen shekarar 2027, wadda za ta tilasta ɗora sakamakon zaɓen akwatuna da na sauran wuraren da ake tattara sakamakon zaɓe.

Akwai kiraye dai dama da suke nuni da cewar akwai buƙatar a bai wa ƴan Najeriya mazauna ƙasashen waje damar yin zaɓe a lokutan zaɓuɓɓukan Najeriya, haka kuma akwai kiraye-kirayen da ke cewa a tilasta wa Hukumar Zaɓe tura sakamakon zaɓe ta na’ura.

Majalissar Sanatocin ta yi nuni da cewar, dole ne a warwarewa Hukumar Zaɓe matsaloli domin ƙarab mata inganci a shirye-shiryenta na gudanar da zaɓuɓɓuka.