Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Santuraki Zai Samarwa Ma’aikatan Jigawa Rancen Noma Da Kiwo Marar Kudin Ruwa

Dan takarar gwamnan Jihar Jigawa karkashin tutar Jam’iyyar PDP, Alhaji Mustapha Sule Lamido, Santurakin Dutse, ya yi alkawarin karawa ma’aikatan gwamnati da ke jihar karfin guiwa wajen shiga harkar sana’ar noma da kiwo domin bunkasa tattalin arzikinsu.

Dan takarar ya yi wannan bayani ne a shafinsa na Facebook, a cikin jerin irin aiyukan da yake alkawarin yiwa al’ummar Jihar Jigawa idan har sun zabe shi a ranar Asabar mai zuwa.

Santurakin Dutsen ya ce, “Ya kamata a samar da wani ƙuduri na ƙarfafa guiwar ma’aikatan gwamnati da kamfanoni su shiga harkar noma a matsayin ƙarin sana’a.

“Gwamnati ta duba yiwuwar ware wasu kuɗaɗe don bada rancen yin noma ga ma’aikata ba tare da kuɗin ruwa ba wanda za a dinga cirewa daga albashinsu a tsawon wani lokaci.”

Dan takarar gwamnan na jam’iyyar PDP ya kara da cewa,  za a tabbatar da cewa iya waɗanda aka tabbatar suna kan tsarin noman ne kaɗai za a ba wannan rance.

Ana yawan kallon ma’aikatan gwamnati a Jihar Jigawa a matsayin masu dogara da iya albashinsu, abin da ke hana wadatar arziki da walwala a jihar a lokuta da dama.

A baya dai ma’aikatan gwamnatin jihar na samun wasu tagomashi daga tsohuwar gwamnatin jihar, abubuwan da gwamnati mai ci ta sossoke saboda matsin tattalin arziki in ji ta.