Ƙungiyar SERAP ta buƙaci Shugaba Bola Tinubu da ya umarci Kamfanin Man Fetur na Najeriya (NNPCL) da ya gaggauta sauƙe farashin fetur da aka ƙara wanda suka kira da ba bisa ƙa’ida ba.
Sun kuma buƙaci Shugaban ya umarci Ministan Shari’a da hukumomin yaƙi da cin hanci su binciki zarge-zargen cin hanci da almubazzaranci a NNPC, musamman game da kashe dala miliyan 300 da suka ce aka karɓa daga Gwamnatin Tarayya a watan Agusta 2024 da kuma bashin dala biliyan 6 da ake bin kamfanin.
SERAP ta ce duk wadanda aka samu da laifin cinhanci da almubazzaranci a NNPC to ya fuskanci hukunci idan akwai ƙwararan hujjojin da za su tabbatar da laifin, tare da ƙwato dukiyar da aka samu ya same ta hanyoyin da ba su dace ba.
A cikin wasikar da SERAP ta aika a ranar 7 ga Satumba 2024, mai ɗauke da sa hannun Mataimakin Daraktan kungiyar, Kolawole Oluwadare, ta bayyana cewa ƙarin farashin fetur ya saɓa wa kundin tsarin mulki da kuma haƙƙin bil’adama na ƙasa da ƙasa da Najeriya ta amince da su.
Ƙungiyar ta jaddada cewa ƴan Najeriya sun daɗe suna fama da rashin adalci game da cinhanci a ɓangaren man fetur wanda ya janyo musu ƙarin kuɗin da suke siyan man.
Wasiƙar ta ci gaba da cewa, maimakon gwamnati ta ɗauki matakan rage talauci da rashin daidaito a ƙasa, tana ƙara matsa wa talakawa lamba ta hanyar barin NNPC ba tare da bibiya ba kan zarge-zargen cin hanci.
SERAP ta bayyana cewa ƙarin farashin fetur ya ƙara jefa talakawan da suka riga suka shiga cikin talauci cikin matsanancin hali, inda ya hana su samun buƙatun rayuwa.