Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

SERAP Ta Nemi A Binciki Zargin Auyo Na Biyan Har Naira Miliyan 3 Don Gabatar Da Ƙudiri A Majalisa

Ƙungiyar SERAP ta yi kira ga EFCC da ICPC su binciki Majalisar Tarayya kan zargin cewa ƴan majalisa na “biyan daga naira miliyan 1 zuwa naira miliyan 3” domin su gabatar da ƙudiri, ko miƙa koke-koke.

Kiran ya biyo bayan zargin da ɗan Majalisar Wakilai, Usman Ibrahim Auyo, ya yi cewa ana “biyan kuɗi” kafin a gabatar da aiki a zauren.

A wasiƙar da Mataimakin Daraktan SERAP, Kolawole Oluwadare, ya rubuta, an kuma roƙi Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, da Kakakin Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas, su miƙa batun ga hukumomin yaƙi da rashawa domin “a gano waɗanda abin ya shafa.”

SERAP ta ce “zargin cewa ƴan majalisa na bayar da rashawa don gabatar da ƙudiri babban keta amanar jama’a ne da kuma rantsuwar aiki.”

Ta ƙara da cewa, “rashawa bai kamata ta taɓa shafar yadda ake gudanar da ayyukan dokoki ko tafiyar Majalisar Tarayya ba,” domin “ba dole ne ƴan majalisa su biya rashawa ba kafin su gabatar da ƙudiri.”

Ƙungiyar ta yi gargaɗin cewa idan shugabancin majalisar “bai ɗauki mataki cikin kwana bakwai ba” za ta ɗauki matakan shari’a “don tilasta bin doka a tsarin samar da maslahar jama’a.”

Auyo kuma ya jaddada zargin nasa da cewa “dole ka biya daga naira miliyan 3, ko miliyan 2 ko miliyan 1 don ka gabatar da ƙudiri, sannan bayan ka gabatar sai ka nemi kamun ƙafa da dukkan mambobi 360 kafin su amince,” yayin da wata ƙungiyar mai suna Good Governance Advocates, ƙarƙashin Kwamared Ahmed Ilallah Hadejia ta ce juyawa ɗan majalissar magana aka yi.