Shekaru biyu da hawan shugaba Bola Ahmed Tinubu kan karagar mulki, tallafin naira biliyan 200 da ya yi alƙawarin bai wa masana’antu da ƙananan ƴan kasuwa domin rage raɗaɗin cire tallafin fetur da dunƙule kuɗin musaya, har yanzu bai tabbata ba sai wata ƴar naira dubu 50 da aka fara rabawa ga ƙananan ƴan kasuwa a watan Afrilun 2024.
Sai dai da yawa daga cikin matsakaitan ƴan kasuwa da masana’antu ba su ga ko sisin kwabo daga babban tallafin da aka yi alƙawarin ba, lamarin da ya janyo gagarumar damuwa da rashin tabbas tsakanin ƙungiyoyin ƴan kasuwa.
A cewar rahoton ICIR, bayan da shugaban ƙasa ya bayyana a ranar 31 ga watan Yuli, 2023, cewa zai ware naira biliyan 75 ga masana’antu da naira biliyan 125 ga MSMEs, an soki yadda aka mayar da alƙawarin zuwa wani sabon tsarin da ba a fara aiwatar da shi ba har sai ranar 22 ga watan Afrilu, 2024.
Ministar Kasuwanci, Masana’antu da Zuba Jari, Doris Uzoka-Anite, ce ta bayyana wannan sabuwar hanya, inda ta ce yanzu masana’antu za su samu har zuwa naira biliyan daya, yayin da kananan ƴan kasuwa za su samu zuwa naira miliyan ɗaya kacal, cikin tsarin rance mai sauƙin ruwa.
WANI LABARIN: Ma’aikatan Internship a Asibitin Koyarwa na Tarayya, Gombe, Za Su Tsunduma Yajin Aiki Saboda Rage Musu Albashi
Sai dai har yanzu ƙungiyoyi kamar MAN, ASBON, NASME da AMEN sun bayyana cewa babu wanda daga cikinsu ko membobinsu ya samu wannan tallafi, inda suka ce abin da suke da shi kawai shi ne kalaman shugaban ƙasa.
Shugaban ASBON, Femi Egbesola, ya ce, “Wasu daga cikinmu sun samu naira dubu 50, amma me hakan ke iya yi a kasuwanci a yau? Kuma har yanzu babu wanda ya samu naira miliyan 5 da aka ce za a bayar gaba ɗaya.”
Shugaban AMEN, Saviour Iche, ya ƙara da cewa, “Gwamnati za ta fito a kafafen yaɗa labarai ta ce an bayar da tallafi, amma dukkan mu shugabanni ba mu san yadda ake bayar da kuɗin ba.”
ICIR ta ƙara da cewa, tsarin da ya kamata ya kawo sauƙi ga harkokin kasuwanci yanzu ya zama hanya mai cike da matsaloli da shakku, inda waɗanda aka yi niyya a taimaka musu ke ƙara rushewa saboda jinkirin gwamnati.
Wannan ya janyo masu fashin baƙi da dama suna tambayar shin mene ne ya faru da wannan alƙawari tun daga shekarar 2023 har zuwa wannan lokacin da muke daf da shiga tsakiyar shekarar 2025.
ICIR