Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Shugaba Tinubu Ya Ce CBN Ya Dakatar Da Maganar Cirar Harajin Kula Da Intanet Kan Asusun Mutane

Wasu majiyoyi da ke da kusanci da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu sun bayyana cewar shugaban ya umarci Babban Bankin Najeriya, CBN da ya dakatar da batun cirar harajin bayar da tsaron intanet ga asusun bankunan ƴan Najeriya.

Majiyoyin sun bayyana cewar, shugaban yana sane da irin halin matsin rayuwar da ƴan Najeriya ke ciki tun daga lokacin da tsare-tsaren tafiyar da tattalin arziƙin Najeriya a gwamnatinsa suka fara bayyana a watan Mayun bara.

Wata majiya da ta buƙaci a boye sunanta saboda rashin izinin yin magana kan batun ta ce, Shugaba Tinubu ba shi da niyyar ƙara jefa ƴan Najeriya cikin ƙunci ta hanyar ɓullo musu da sabbin haraje-haraje.

Wani babba jami’i a Fadar Shugaban Ƙasa ya bayyana wa jaridar PUNCH cewar, shugaban ƙasa ya damu da halin da ƴan Najeriya ke ciki, sannan ba shi da niyyar ƙara ƙaƙaba musu wata wahalar da zata ƙara musu ƙuncin da suke ciki.

Ya ce, wannan ne dalilin da ya sa shugaban ya buƙaci CBN ya dakatar da aiwatar da dokar tare da sake duba ta.

Wata majiyar ta daban a Fadar Shugaban Ƙasar kuma ta ce, wannan mataki na Tinubu ya samo asali ne daga cecekucen da maganar sabon harajin ta jawo a faɗin ƙasa.