Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Shugaban Karamar Hukumar Hadejia Ya Yi Kira Da A Rika Taimakawa Mata

Shugaban Karamar Hukumar Hadejia, Hon. Abdulkadir Umar TO ya yi kira ga shugabanni, ƴan siyasa da masu hannu da shuni da su rika bai wa mata taimako, wajen samar musu da jari da zasu na yin sana’oi inda ya ce, ta haka ne za su samu damar dogara da kansu.

Shugaban Karamar Hukumar ya yi wannan kiran ne lokacin da kungiyar mata ta Women Media Crew suka karramashi da bashi lambar yabo, saboda irin aiyukan da yake yi a Karamar Hukumar Hadejia.

Kungiyar Matan sun bayyana waɗannan aiyuka da cewar sun kawo kawo gagarumin canji da kawo cigaba a ƙaramar hukumar.

Matan sun bayyana shugaban a matsayin wanda ya fi kulawa da tallafawa mata a tarihin Haɗejia, domin kuwa shine shugaban da ya fara kaddamar da bai wa mata tallafi domin su samu jarin da zasu riƙe kansu.

Hon. Abdulkadir Umar TO, ya ja hankalin mutane da shugabanni cewa mata, musamman wanda suka rasa mazajensu, akasarin su suna cikin yanayi na bukatar taimako, mussaman ma in an yi la’akari da yanayin da a ke ciki a halin yanzu inda ya ƙara da cewar, akasarin yanayi na munanan halin da mata suke fadawa ciki, suna shiga ne a sanadiyar talauci da rashin aikin yi.