Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Shugabannin CPC Sun Ce Suna Yin APC Ne Kawai Saboda Buhari, Duk Da Cewa An Mayar Da Su Saniyar Ware

A daidai lokacin da siyasa ke fara ɗaukar zafi gabanin zaɓen 2027, tsoffin shugabannin jihohi na jam’iyyar CPC da ta haɗu da wasu don kafa APC sun bayyana cewa sun ci gaba da kasancewa a jam’iyyar ne saboda biyayya ga tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari.

A cikin wata sanarwa da Sakataren ƙungiyar, Sulaiman Oyaremi, ya fitar ranar Lahadi, sun ce kodayake suna fuskantar wariya a cikin jam’iyyar, sun yanke shawarar ci gaba da zama a APC tare da Buhari, domin su goyi bayan shugabancin Bola Tinubu da kuma tabbatar da haɗin kai.

“Mun amince gaba ɗaya cewa muna tare da shugabanninmu, musamman tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari,” in ji sanarwar, yana mai cewa suna so su ga an gina APC da kowa zai ji daɗin kasancewa a cikinta.

WANI LABARIN: Jinkirin Bayar Da Rancen Kuɗin Makaranta Yana Ta’azzara Rayuwar Ɗalibai

Sun bayyana rashin jin daɗinsu da yadda ake watsi da su wurin raba muƙamai da kuma sanya su cikin tsare-tsaren jam’iyya, duk da irin gudummawar da suka bayar tun lokacin da aka kafa APC.

“Wasu daga cikinmu mun daɗe muna jan ragamar jam’iyya tun lokacin CPC, amma yanzu muna ganin an yi watsi da mu, alhali mun taka rawa wajen nasarar jam’iyya,” in ji su.

Duk da haka, sun jaddada aniyar su ta taimakawa wajen gina jam’iyya mai ƙarfi da adalci, inda suka buƙaci shugabannin APC su duba ƙorafin da ke cikin gida domin kaucewa rikicin cikin gida a jam’iyyar.

Sun kuma buƙaci shugabannin jam’iyya su duba rawar da suke takawa da kuma sake nazarin tsarin rabon muƙamai da ba da dama ga kowane ɓangare na jam’iyyar.