Gwamnatin Tarayya ta gayyaci wasu shugabannin jami’o’i da kuma Babban Daraktan Asusun Rancen Dalibai na Ƙasa (NELFund) domin tattauna zargin karkatar da kuɗaɗen da aka ware don tsarin bayar da rancen karatu ga ɗalibai.
Wannan matakin ya biyo bayan rahoton da ya bayyana cewa kusan jami’o’i 51 sun yi wasu haramtattun tsakure-tsakure daga cikin kuɗaɗen rance na NELFund, wanda hakan ya jawo Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (ICPC) fara bincike kan lamarin.
A cewar sanarwar da ma’aikatar ilimi ta fitar, ta ce za a gudanar da taron gaggawa a ranar 6 ga Mayu 2025 tare da shugabannin jami’o’in da abin ya shafa da kuma shugaban NELFund domin zurfafa bincike da tabbatar da gaskiya da adalci.
KARANTA WANNAN: Sama Da Mutum Dubu Sun Kamu Da Cutar Amai Da Gudawa A Najeriya, Wasu Sun Mutu, In Ji NCDC
“Taron zai mayar da hankali wajen binciken al’amura, tabbatar da cikakken sauƙe nauyi, tare da tabbatar da ƙudirin Ma’aikatar na rashin sassauci kan almundahana a ɓangaren ilimi,” in ji sanarwar da Boriowo Folasade, Daraktan Yaɗa Labarai na Ma’aikatar, ya fitar.
Ministan Ilimi, Olatunji Alausa, ya bayyana zargin da cewa “abin takaici ne ƙwarai” kuma zai iya zama saɓawa amana idan an tabbatar da gaskiyarsa.
“Idan hakan ya tabbata, to hakan babban saɓo ne ga amanar jama’a da kuma cin amana ga ƙudirin gwamnati na samar da daidaitacciyar damar samun yin ilimi,” in ji Ministan.
Ma’aikatar ta ce don tabbatar da gaskiya da ƙarfafa sahihanci, za ta ƙaddamar da shafin bibiyar bin doka tare da Athena Centre da kuma samar da ma’aunin duba gaskiyar jami’o’i na shekara-shekara, domin wayar da kan jami’o’i da ba da horo ga ma’aikatan kula da kuɗaɗe da ICT domin ƙirƙirar dandalin bayyanawa jama’a duk wasu bayanai na kuɗi.