Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya jinkirta shirin karɓar katin shaidar zama ɗan jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), a daidai lokacin da ake raɗe-raɗin tsohon Shugaba Goodluck Jonathan na shirin yin takarar shugaban ƙasa a 2027 ƙarƙashin jam’iyyar.
Atiku, wanda ya fice daga jam’iyyar PDP bayan dogon rikicin cikin jam’iyyar da ya ƙi ci ya ƙi cinyewa, an tsara zai karɓi katin ADC ne a garin Jada na jihar Adamawa, amma an ɗage bikin ba tare da bayyana dalili ba.
Shugaban ADC na jihar Adamawa, Shehu Yohana, ya ce Atiku ya faɗa masa a waya cewa an ɗage taron zuwa nan gaba a watan Agusta ko ma Satumba saboda wasu gwamnoni daga APC na shirin sauya sheƙa zuwa ADC.
Wani babban jigon jam’iyyar a matakin ƙasa ya bayyana cewa jinkirin na iya zama saboda rikicin tasiri tsakanin Atiku da tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na Labour Party, Peter Obi, wanda ya ce ya mamaye tsarin jam’iyyar a kudu.
Rahotanni sun nuna cewa ADC na tattaunawa a asirce da Jonathan, inda wani jigo ya tabbatar da cewa “muna samun bayanai masu kyau daga gare shi” kuma ba zai yi takara ƙarƙashin PDP ba saboda tasirin Nyesom Wike.
Atiku ta bakin mai magana da yawunsa, Paul Ibe, ya musanta cewa yana jin tsoron wani, yana mai cewa “a demokaraɗiyya, idan da yawa ma su shiga tseren, hakan ne me kyau”.
Wani jigo na ADC ya zargi gwamnatin Bola Tinubu da ƙulla makirci don tarwatsa burin Atiku a jam’iyyar, yana mai cewa APC “na tsoron ganin shi a takardar kaɗa ƙuri’a a 2027”.
Rahotanni kuma sun bayyana cewa wasu cikin ADC suna nuna matsin lamba ga shugabanninsu da su bar jam’iyyar idan har rikicin bai kau ba.
Haka kuma, ana zargin APC na ƙoƙarin shawo kan Obi da wasu ƴan kudu su shiga PDP, saboda sun san cewa Tinubu zai fi ƙarfi idan Atiku bai tsaya takara ba.
Kakakin riƙon ƙwarya na ADC, Bolaji Abdullahi, ya ce za su yi ƙoƙarin hana duk wata fitina daga waje, yana mai cewa dole ne su kifar da APC a 2027.
Rikicin cikin gida a ADC ya fara ne tun bayan naɗa David Mark a matsayin shugaban jam’iyyar, inda wasu tsofaffin shugabannin jihohi ke ƙalubalantar jagorancinsa.
Duk da haka, Abdullahi ya ce waɗanda ke tayar da ƙura suna yi ne domin neman kulawa da samun kuɗi daga masu hannu da shuni.
Wannan jinkiri na Atiku da raɗe-raɗin shigar Jonathan na iya canza lissafin siyasar Najeriya kafin babban zaɓen 2027, lamarin da zai ƙara shigar da al’amuran siyasar ƙasar cikin rashin tabbas.