Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Sojoji Sun Kashe Ƴan Bindiga 3, Sun Ƙwato Makamai A Kaduna

Rundunar sojojin Najeriya ta ce dakarunta da ke 1 Division sun kashe ƴan bindiga uku tare da ƙwato makamai da sauran abubuwa a Ƙaramar Hukumar Chikun ta Jihar Kaduna.

A wata sanarwa da Musa Yahaya, mai riƙon Mataimakin Darakta kan Hulɗa da Al’umma na Sojoji a 1 Division ya ce, sojojin sun ƙwato bindiga AK-47, da bindigogi yin gida AK-47 guda uku, zaren jakar harsasan AK-47 guda bakwai da kuma babura takwas a lokacin samamen da suka yi.

Sanarwar ta ƙara da cewa, sojojin sun kuma ƙwato harsasai yin gida, wayoyin hannu guda shida da kuma kayan maye.

Sanarwar ta kuma ce, Babban Kwamnadan 1 Division, Manjo Janar BA Alabi ya yabawa sojojin bisa nasarar da sojojin suka samu, sannan kuma ya yi kiransu da su ƙara jajircewa har sai sun kawo ƙarshen ɓatagarin.