Rundunar Sojojin Najeriya ta tabbatar da kashe aƙalla ƴanta’adda 59 tare da kama wasu 88, sannan kuma sojojin sun samu nasarar kama masu garkuwa da mutane 10 da adadi mai yawa na masu satar ɗanyen mai.
Mai Magana da Yawan Rundunar Tsaron, Major General Edward Buba ne ya tabbatar da labarin, ya kuma ce rundunar ta yi samame da dama a yankuna shida na Najeriya domin magance matsalar tsaro.
Labari Mai Alaƙa: Ƴan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Ƴanmata Da Zawarawa 23 A Zamfara
Ya ce, zuwa ranar Juma’a 28 ga watan Yuli, sojojin sun samu nasarar kashe ƴanta’adda 59, sun kuma kama wasu ɓatagarin su 88, da masu garkuwa da mutane 10, da ƴanbindiga 20 da kuma masu satar ɗanyen mai su 19.
Major Janar Buba ya kuma ce, sojojin sun samu nasarar kuɓutar da waɗanda akai garkuwa da su har su kimanin 88, yayinda sojojin suka sami nasarar ƙwato bindugu da harsasai da dama da kuma ɗanyen man da aka sace mai yawan ganga sama da dubu ɗari uku.
