Koda yake gwamnati na kokarin kawo sauyi ga tsarin gyaran hali a Najeriya, alkaluman Hukumar Kula da Fursunoni sun nuna cewa daga cikin mutane 79,474 da ke cikin gidan yari a kasar nan, mutum 52,893, kimanin kaso 67 cikin 100, ba a yanke musu hukunci ba har yanzu, yayin da 51,407 daga cikinsu maza ne, mata kuma 1,486.
A cewar Oluyemi Adetiba-Irija, lauya kuma shugabar Headfort Foundation, a wata hira da ta yi da PREMIUM TIMES, ta bayyana cewa akwai mutum mai suna God’swill wanda ya shafe shekara 11 a gidan gyaran hali na Ikoyi ba tare da an gurfanar da shi gaban kotu ba.
Ta ce “a Ikoyi, da aka gina don mutane 800, yanzu ana cunkushe da fiye da 3,000 zuwa 3,500 a kowane lokaci, haka abin yake a Kirikiri da sauran manyan gidajen yari,” lamarin da ke nuna irin taɓarɓarewar da tsarin ya shiga.
WANI LABARIN: Kamfanin Meta Zai Dakatar Da Facebook Da Instagram A Najeriya
Ko da yake dokokin kamar ACJA sun tanadi hanzarta yin shari’a, amma rashin isassun alƙalai da cunkoso a kotuna na janyo tsaikon shari’o’i, tare da rashin isassun motoci ko man fetur don kai fursunoni kotu.
Ta ce “wannan ne yasa wasu ke shafe shekaru da dama cikin kurkuku fiye da lokacin da za su kwashe in an same su da laifi.”
Duk da cewa Jihar Lagos ta fara tsarin sauraron shari’a ta yanar gizo da bin diddigin shari’o’i ta na’ura, amma har yanzu ba a aiwatar da su yadda ya kamata ba.
Oluyemi ta ƙara da cewa “koda kuwa ba da gangan ake jinkirta shari’a ba, amma rashin tsarin da ya dace da rashin haɗin kai tsakanin ƴansanda da kotuna na ƙara dagula lamarin, sannan gwamnatin tarayya ce har yanzu ke da alhakin kula da fursunoni, ba jihohi ba.”