Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

‘Tana Kirana Ne Kaɗai Idan Tana Buƙatar Kuɗi,’ In Ji Wanda Yai Wa Budurwarsa Kisan Gilla

Wani matashi ɗan shekara 45 mai suna Bankole Oginni, wanda ƴansanda suka kama a Jihar Ondo bisa zargin kashe tsohuwar budurwarsa, ya bayyana dalilan da suka sa ya aikata aika-aikar.

Wanda ake zargin dai ya aikata laifin ne a gidansa da ke yankin Danjuma a birnin Akure na Jihar ta Ondo.

An dai kama Bankole ne bayan ya fafe cikin masoyiyar tasa ya zazzaro hanjinta ya kuma cire al’aurarta.

Haka kuma ana zarginsa da ɗaɗɗaure budurwar tasa a hannaye da ƙafafunta, sannan kuma ya kwara mata ruwan zafi.

Ƴansanda ne suka gano aika-aikar da Bankole ya yi, inda kuma rahotanni ke cewa wanda ake zargin ya bayyana musu abun da ya faru da tsakaninsa da budurwar tasa.

Ya faɗa musu cewa, budurwar tasa ta kira shi ne ranar wata Asabar tana buƙatar temakon kuɗi a wajensa, sai ya ce mata su haɗu a gidan babansa.

Ya ƙara da cewa, duk lokacin da take da buƙatar kuɗi da ma yana ce mata ta je su haɗu a gidan babansa, sai a wannan lokacin ma ta je ya kuma kawo mata lemon kwalba mai sanyi amma ta ƙi sha.

Ya ce, to bayan haka ne sai ta faɗi a sume, inda ya rasa mai zai yi mata, sai kawai ya kwara mata ruwan zafi ko zata farfaɗo.

To sai dai kuma bayan duk wani ƙoƙari da ya yi na ta farfaɗo bai kai ga nasara ba, cikin tsoro, sai kawai ya farka cikinta ya zaro hanjinta domin ya rage mata nauyi don saka ta a cikin buhu.

Ya kuma ce, ya ɗaɗɗaureta ne saboda ya ji sauƙin jefar da ita.

Mai Magana da Yawun Ƴansandan Jihar, Funmi Odunlami ya ce, ƴar wadda aka yi wa kisan gillar ce ta sanar da ƴansandan abun da ya faru.

Odunlami ya ƙara da cewa, ƴar marigayiyar ta ce musu, wanda ake zargin ya gayyaci mahaifiyarta ne, daga baya kuma sai kawai ta ga ba ta dawo ba, bayan an kikkira wayarta a kashe.

To shine ta bi mahaifiyar tata har gidan, sai ta samu gawarta an ɗaɗɗaure hannayenta da ƙafafunta sannan an fafe cikinta an kwashe hanjinta.

Odunlami ya ce, za a gurfanar da Bankole a gaban kotu bayan ƴansanda sun kammala bincikensu.