Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Tanaden-Tanaden Tinubu Na Sauƙaƙawa Ƴan Najeriya Ba Zasu Magance Komai Ba – Ƙungiyar Ƴan Kasuwa

Haɗaɗɗiyar Ƙungiyar Ƴan Kasuwa, TUC, ta bayyana cewa tanade-tanaden da Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya bayyana a jawabinsa cewar ya yi domin rage raɗaɗin janye tallafin man fetur ba zasu magance komai ba.

Da yake jawabi ga manema labarai bayan zaman Kwamitin Shugaban Ƙasa kan Samar da Sauƙi ga Ƴan Ƙasa, Shugaban Ƙungiyar TUC, Festus Osifo, ya bayyana shirin tallafin da shugaban ƙasa ya sanar a matsayin waɗanda suka yi matuƙar kaɗan.

Da yake magana kan abubuwan da aka tattauna a zaman, Osifo ya ce, Gwamnatin Tarayya ta buƙace su da su dakatar da zanga-zangar da suka shirya farawa yau, inda ya ce amma sun nuna musu cewar zasu zauna a jiyan, yayinda bayan zaman za a ji matakin da suka ɗauka.

Lokacin da yake magana da ƴanjaridar da ke Fadar Shugaban Ƙasa, Osifo ya ce, motocin bas 3000 da Tinubu yai alƙawari ba zasu isa komai ba a Najeriya.

Ya ƙara da cewar zasu matsa wajen ganin an samar da motocin bas da suka kai 30,000 ko 40,000 saboda a ganinsa, yawan hakan ne zai iya isar Najeriya.

Shugaban na TUC ya ce, duk da cewar ƙungiyoyin ƙwadago na buƙatar a ƙara mafi ƙarancin albashi domin ai maganin matsin tattalin arziƙi da ya samo asali daga janye tallafin man fetur, wannan buƙata zata ɗau lokaci, tun da har yanzu ba a samar da kwamiti kan hakan ba.

Ya ce akwai tsarin da ƙungiyoyin ƙwadagon suka gabatar na samun ƙaruwar albashin ma’aikata ba tare da dogon surutu ba, inda ya ce, wasu jihohin sun fara inda wasu ke biyan mafi ƙarancin albashi na naira 40,000, sai dai ita Gwamnatin Tarayya a nata ɓangaren ba ta ce komai ba.