Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

TASHIN BAMA-BAMAI: Ƴan Boko Haram Sun Hallaka Fasinjoji 9 A Borno

Aƙalla mutane tara ne suka mutu sakamakon fashewar bama-bamai da aka dasa a wata tashar mota da ke kauyen Mairari a ƙaramar hukumar Guzamala ta jihar Borno, kamar yadda rahoton Daily Trust ya tabbatar, tare da bayani daga Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Borno, Abdulkarim Lawan.

A cewar ɗan majalisar, “Abin takaici ne yadda wasu daga cikin mazabata masu juriya guda tara suka rasa rayukansu sakamakon fashewar bama-bamai da aka dasa a tashar mota yayin da suke jiran hawa mota a kauyen Mairari, ranar Lahadi. Allah Ya gafarta musu Ya kuma sa Aljanna Firdausi ta zama makomarsu.”

Lawan ya bayyana cewa mutane da dama sun jikkata a harin, kuma tuni aka garzaya da su asibiti domin samun kulawar gaggawa.

Ya ce ƙauyen Mairari shi ne kaɗai ƙauyen da aka yi ƙoƙarin sake maido da ikon gwamnati sau biyu a Guzamala, amma ya sake zama kufai saboda hare-haren Boko Haram da ISWAP.

KARANTA WANNAN MA: Bayan Karɓar Maƙudan Kuɗin Fansa, Ƴan Bindiga Sun Halaka Wani Shugaban APC

“Yawancin mutanen da ke ƙauracewa suna zaune a Monguno da Maiduguri, amma suna komawa Mairari domin yin noma,” inji shi, yana mai bayyana cewa, “Wasu ƴan ta’adda da ke bibiyar motsin su sun dasa bama-bamai a tashar mota inda suka tarwatse yayin da ake jiran mota.”

Lawan ya bayyana harin a matsayin mummunan abu da babu tausayi a cikinsa, tare da kiran rundunar soji da ta ƙwace Guzamala daga hannun ƴan ta’adda domin dawo da shugabanci na gari.

“Na san sabon kwamandan rundunar Operation Hadin Kai, Manjo Janar Abdulsalam Abubakar, da sojojinsa suna aiki tuƙuru wajen yaƙi da Boko Haram da ISWAP, amma har yanzu Guzamala na ƙarƙashin ikon su,” inji shi.

Har ila yau, rundunar sojin ƙasa ta Najeriya ta bayyana kashe wani kwamandan ISWAP mai suna Abu Fatima wanda aka sanya ladan Naira miliyan 100 kansa, yayin da mai ba da shawara kan harkokin tsaro na ƙasa, Nuhu Ribadu, ya bayyana cewa sojojin sun kashe sama da ƴan ta’adda 13,000 a yankin Arewa maso Gabas cikin shekaru biyu.

Sai dai duk da haka, ƙungiyoyin Boko Haram da ISWAP na ci gaba da kai hare-hare kan fararen hula da jami’an tsaro, inda rahoton PREMIUM TIMES ya ce mutane 1,457 aka kashe a yankin cikin shekaru biyu na mulkin Bola Tinubu, tare da sace wasu fiye da 900 a wannan lokaci.