Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Tashin Hankali A PDP: Shugabancin Jam’iyyar Ya Barranta Kansa Da Batun Neman Komawar Jonathan Da Peter Obi

Tashin hankali ya sake kunno kai a jam’iyyar PDP yayin da ake tunkarar zaɓen shugaban ƙasa na 2027, bayan labarin cewa wasu manyan ƴan jam’iyyar na ƙoƙarin mayar da tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan da tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi, cikin jam’iyyar.

A yau Alhamis, za a ƙaddamar da kwamitin rabon kujerun NWC da na rabon kujerun zaɓen 2027 a Abuja, duk da cewa ba kowa ke goyon bayan wannan shirin ba.

Wani jigon kwamitin NEC na jam’iyyar ya bayyana cewa, “Za mu karɓi Jonathan da Obi, amma da zuciya biyu, domin sun bar jam’iyyar a lokacin da ake buƙatarsu sosai.”

Sai dai wasu mambobin NEC na ganin PDP na da isassun ƴan takara masu ƙima kamar gwamnan Oyo, Seyi Makinde, da gwamnan Bauchi, Bala Mohammed.

Babban sakataren yaɗa labaran PDP, Debo Ologunagba, ya bayyana cewa, “A jam’iyyarmu akwai mutane da dama da za su iya zama shugaban ƙasa, kuma muna da tsari a dukkan jihohi da mazaɓu.”

A gefe guda, APC ta yi tsokaci ta bakin daraktan yaɗa labaranta, Bala Ibrahim, cewa PDP jam’iyya ce “mai fama da ciwon zuciya” wadda ba za ta iya tsallakewa ba a 2027.

Rahotanni sun nuna cewa, bai taɓa zama shirin shugabancin PDP ba, batun tuntuɓar Jonathan da Obi, sai dai wasu mutane ne ke yi a matsayin kansu ba jam’iyya ba.

Wasu jiga-jigan PDP na ganin ana neman Jonathan ne saboda “sauƙin tallata shi” yayin da wasu ke cewa babu wani wanda ya fi ƙarfin bin ƙa’idojin jam’iyya.

Duk da rarrabuwar kawunan nan, PDP na shirin taron zaɓen shugabannin jam’iyyar a Ibadan a watan Nuwamba, tare da kiran duk wanda zai dawo da ya kasance mai cikakkiyar biyayya ga jam’iyyar.