Rahoton da Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS) ta fitar ya bayyana cewa tattalin arziƙin Najeriya ya ƙaru da kaso 3.13 cikin 100 a watanni uku na farkon shekarar 2025.
Wannan adadi ya fi kaso 2.27 cikin 100 da aka samu a lokaci iri ɗaya a shekarar 2024, wanda ke nuni da ci gaba a ɓangaren kasuwanci da masana’antu.
Rahoton ya nuna cewa sassan da suka fi taka rawa sun haɗa da ɓangaren ayyuka, masana’antu, da noman zamani.
Hakanan, an sabunta ƙididdigar adadin kuɗin GDP daga shekarar 2019 zuwa naira tiriliyan 205, wanda ya haura da kashi 41.7 idan aka kwatanta da shekarar 2014.
WANI LABARIN: Kamfanonin Wutar Lantarki Zasu Katse Wutar Ƙasa Gaba Ɗaya, Sun Bayyana Dalili
Shugaban NBS, Adeyemi Adeniran, ya bayyana cewa wannan sabon adadi ya samo asali ne daga sabon tsarin ƙididdiga na ƙasa.
Ya ƙara da cewa noman zamani da kamfanonin sadarwa da masana’antu sun taka muhimmiyar rawa wajen haɓaka GDP a Najeriya.
Sauran sassa da suka ba da gudummawa sun haɗa da man fetur da kuma iskar gas.
Rahoton na zuwa ne a daidai lokacin da Najeriya ke fama da hauhawar farashi da raguwar ƙarfin iya siyayya a ɓangaren al’ummarta.
Masana tattalin arziƙi sun bayyana wannan ci gaba a matsayin wani abin ƙwarin gwiwa duk da ƙalubalen da ƙasar ke fuskanta.