Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Tinubu Ya Naɗa Hakeem Baba Ahmed A Matsayin Mai Bayar Da Shawara Na Musamman

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya naɗa Mai Magana da Yawun Ƙungiyar Dattawan Arewa, Dr. Hakeem Baba-Ahmed a matsayin Mai Bayar da Shawara na Musamman a Kan Harkokin Siyasa a Ofishin Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima.

Baba-Ahmed wanda yaya ne ga wanda yai wa Peter Obi takarar mataimakin shugaban ƙasa a zaɓen 2023 ƙarƙashin tutar jam’iyyar Labour Party ya bayyana naɗin na sa ne a shafinsa na X a yau Litinin.

KARANTA WANNAN: Tinubu Ya Naɗa Madadin Garba Shehu Da Wasu Muƙaman Da Dama

Baba-Ahmed ya ce, an girmama shi wajen ba shi damar bayar da gudunmawarsa a gina ƙasa.

Ya rubuta a shafin cewa, “Lokaci ya yi da zan bayyana shi ga jama’a cewar, na karɓi kiran da akai min na na yi aiki a matsayin Mai Bayar da Shawara kan Harkokin Siyasa ga Mataimakin Shugaban Ƙasa.

“Yanzu ba lokacin zaman kan katanga ba ne ko soke-soke alhalin za ka iya zama mai amfani wajen daidaita lamuran ƙasa. An mutumtani an karrama ni. Don Allah ku taya ni da Najeriya da addu’a.”