Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Tinubu Ya Sanar Da Ƙarawa Ƙananan Ma’aikata Naira Dubu 25 A Tsawon Watanni 6

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ce, a watanni shida masu zuwa, ƙananan ma’aikata za su sami ƙarin naira dubu ashirin da biyar a duk wata.

Shugaban ƙasar ya bayyana hakan ne a jawabinsa na murnar cikar Najeriya shekarun 63 da samun ƴancin kai.

Tinubu ya ce, bisa la’akari da tattaunawar da ake da ƙungiyar ƙwadago, gwamnati ta zo da ƙarin albashi da zai ƙarawa mafi ƙarancin albashi yawa ba tare da an samu hauhawar farashi ba.

ƘARIN LABARI: Najeriya Na Neman Sabon Bashin Naira Tiriliyan 1.2 Da Wasu Basussukan Daga Bankin Duniya

Shugaban ya bayyana hakan ne a lokacin da yake bayani kan abubuwan da aka tanada ga ƴan ƙasa domin rage raɗaɗin janyen tallafin mai da kuma daidaita canjin kuɗaɗen ƙasashen waje.

Tinubu ya ce, gwamnatinsa na yin duk mai yiwuwa wajen ganin ta samar da sauƙi da bunƙasa tattalin arziƙi da kuma magance hauhawar farashi da ma bunƙasa samar da kayayyaki da tsaron rayukan al’umma da dukiyoyinsu.