Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Tinubu Ya Yabi Nasarar Zaɓen Cike-Gurbi A Jihohi 12, Ya Godewa Ƴan Najeriya Bisa Nuna Yarda Da APC

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya murnar nasarar zaɓen cike-gurbi na Asabar, 16 ga Agusta, a mazaɓu 16 a jihohi 12, kamar yadda fadar shugaban ƙasa ta bayyana a sanarwar da ta fitar.

Ya yabawa Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) kan gudanar da zaɓe cikin lumana “hitch-free,” wanda aka ce “a yawancinsa ba a samu tashin hankali ba.”

Bisa sakamakon da INEC ta bayyana, APC ta lashe kujeru 12, APGA biyu, PDP ɗaya, NNPP ma ɗaya.

Tinubu ya kuma taya sabon Shugaban APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, murna da “babbar nasarar farko,” tare da godewa gwamnoni da sauran shugabannin jam’iyyar.

A cewarsa, “Nentawe Yilwatda ya nuna iya shugabanci, ya kuma nuna irin nasarar da za a samu yayin da aka gabatar da sanannun ƴan takara aka kuma samu haɗin kan jagororin jam’iyya.”

Ya ƙara tabbatarwa magoya bayan jam’iyyar APC cewa, “Zuwa ga dukkan magoya bayan APC da masu zaɓe, mun gode muku bisa ƙwarin gwiwar da kuka ba mu . . . Makomar da muke samarwa ita ce Najeriya mai kyau, mai cikakken tsaro kuma mai cigaba. Da izinin Allah zamu kai ku ga can.”

Sanarwar da Bayo Onanuga ya rattaba wa hannu a ranar Lahadi, 17 ga Agusta, 2025, ta yi kira ga jam’iyyu su ci gaba da tafiya a kan “kyakkywan tsarin gwagwarmaya, takara ta adalci da dattako” domin ɗorewar demokaraɗiyya.