Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Tinubu Zai Haɗe, Raba, Ruguje Da Ƙirƙirar Wasu Ma’aikatun A Gwamnatin Tarayya

Biyo bayan gabatar da rukuni na farko na waɗanda shugaban ƙasa ke son naɗawa ministoci, alamu sun nuna cewa, Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu zai  sake fasalin wasu ma’aikatun Gwamnatin Tarayya ta hanyar haɗe wasu, ƙirƙirar wasu da kuma ruguje wasu.

Binciken da jaridar PUNCH ta yi ya nuna cewa, matakin da shugaban ƙasar zai ɗauka ya samo asali ne daga shawarwarin rahoton Stephen Oronsaye kan sake fasalin tsarin aikin gwamnati.

Bincike ya nuna cewa, Ma’aikatar Ilimi, Ma’aikatar Matasa da Ci Gaban Wasanni, Ma’aikatar Noma da Raya Karkara, Ma’aikatar Kare Ibtila’i da Samar da Ci Gaban Al’umma na cikin waɗanda za a sakewa fasalin, abin da zai haifar da ƙirƙirar wasu ma’aikatun sabbi.

Binciken da wakilin PUNCH yai a jiya Juma’a ya nuna cewa, akwai shirye-shiryen raba Ma’aikatar Ilimi, inda za a mayar da ita guda biyu da suka haɗa da Ma’aikatar Ilimin Manyan Makarantu da kuma Ma’aikatar Ilimi a Matakin Farko.

Haka ita ma Ma’aikatar Aiyuka da Gidaje za a raba ta zuwa Ma’aikatar Aiyuka wadda zata mayar da hankali kan titunan tarayya da kuma Ma’aikatar Gidaje wadda za a yi amfani da ita wajen bunƙasa tattalin arziƙi.

Labari Mai Alaƙa: DA ƊUMI-ƊUMI: Tinubu Ya Miƙawa Sanatoci Sunayen Ministoci, Sunan Badaru Ne Daga Jigawa

An kuma gano cewar, Ma’aikatar Kula da Walwalar Al’umma, Samar da Ci Gaban Ɗan’adam da Kare Ibtila’i za a sake mata fasali ta koma Ma’aikatar Bunƙasa Rayuwar Ɗan’adam.

Ita ma Ma’aikatar Kula da Harkokin Sufuri za a raba ta gida biyu ta koma Ma’aikatar Kula da Harkokin Sufurin Jirgin Ƙasa da Kuma Ma’aikatar Kula da Sufurin Cikin Ruwa.

Ita kuma Ma’aikatar Yaɗa Labarai zata koma Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Ƴan Ƙasa.

Za a kuma ƙirƙiri sabuwar Ma’aikatar Bunƙasa Ma’adanai da Sarrafa Ƙarafa.

Za a mayar da Ma’aikatar Noma ta tsaya a iya Ma’aikatar Noma, yayinda za miƙa ɓangaren Raya Karkara zuwa Ma’aikatar Bunƙasa Rayuwar Ɗan’adam.

Wasu majiyoyi daga Fadar Shugaban Ƙasa sun nuna cewa, Ma’aikatar Kasafi da Tsare-tsaren Ƙasa za a sake mata fasali inda za a mayar da ɓangaren kasafi zuwa Ma’aikatar Kuɗi, sai kuma ɓangaren tsare-tsare ya koma sabuwar Ma’aikatar Ƙididdiga ta Ƙasa da za a ƙirƙira.

Ita kuma Ma’aikatar Ciniki da Masana’antu za a ɗauke ɓangaren cikinikin a mayar da shi Ma’aikatar Kasuwanci da Sanya Hannun Jari, yayinda ɓangaren masana’antu zai koma sabuwar Ma’aikatar Samar da Aikin Yi da Masana’antu da za a ƙirƙira.