Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Tsarin Shugaban Ƙasa Ba Shi Da Amfani A Najeriya, A Koma Tsarin Firaminista, In Ji Wani Ɗan Majalissa

Wani ɗan Majalissar Wakilai mai suna Abdussamad Dasuki ya ce, tsarin da ake kai na shugaba mai cikakken iko a Najeriya ba ya temakon Najeriya, ya kamata a yi watsi da shi a dawo tsarin firaminista irin wanda aka yi a jamhuriya ta farko.

Ɗan Majalissar mai wakiltar mazaɓar Kebbe/Tambuwal daga Jihar Sokoto, ya bayyana hakan ne a shirin gidan talabijin na Channels da aka watsa a yau Juma’a.

Ya ce, Najeriya tana cikin rikicin makoma, kuma kamar gidan da ba shi da kyakkyawan ginshiƙi, tsarin da ake bi a yanzu ba ya yi wa ƴan Najeriya amfanin komai, inda masu zartarwa tun daga kan shugaban ƙasa ke gudanar da komai su kaɗai.

Dasuki ya ce, “Abubuwa ba sa aiki a Najeriya, wannan ba abun ɓoyewa ba ne. Wannan (yunƙuri na komawa tsarin firaminista) ba a wannan majalissar aka fara ba, waɗansunmu da ke Majalissa ta 8 sun yarda da cewar akwai matsala a kan tsarin da ake kai.

“Tsarin yana da matsala. Waɗansu zasu ce wannan matsalar Najeriya ce, da ƴan Najeriyar da komai, amma tsarin a kan kansa ya ba ku ƙarfi mai yawa, kuma wannan ƙarfin ikon yana lalata abubuwa.

“Iyayenmu suna da hangen nesa da suka yarda da cewar Najeriya ƙasa ce ta mutane daban-daban saboda haka ya kamata komai ya zama don mutane daban-daban. Ya kamata mu samu yanayin da ko da manyanmu ne zasu zauna su fito mana da wani tsari da zai fi dacewa  da mu.”

Tun a tsakiyar watan Fabarairu na bana ne, maganganu kan mayar da Najeriya tsarin firaminista ya ɓarke a Majalissar Wakilai, inda wasu ƴan majalissar su 60 suka buƙaci a gyara Kundin Tsarin Mulkin Najeriya inda za a koma tsarin firaminista daga tsarin shugaban ƙasa mai cikakken iko.

Ƴan majalissar sun ce, komawa tsarin firaminista ya zama dole saboda a rage kuɗin gudanar da gwamnati da yake kassara tafiyar ƙasar nan.