Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

TSARO A NAJERIYA: Shekaru Biyun Farko Na Bola Tinubu, Matsalar Tsaro Na Ci Gaba Da Fin Ƙarfin Gwamnati

Bayan cika shekara biyu da Bola Ahmed Tinubu ya hau kujerar shugabancin Najeriya tare da alƙawarin daidaita harkar tsaro a cikin shirin sa na Renewed Hope Agenda, matsalolin tsaro sun ci gaba da ta’azzara a faɗin ƙasar, lamarin da ke barazana ga zaman lafiya da cigaban ƙasa.

A cikin jawabin rantsar da shi a ranar 29 ga Mayu, 2023, Tinubu ya ce, “Tsaro shi ne babban abin da gwamnatinmu za ta mayar da hankali a kai, domin ba za a iya samun cigaba ko adalci a cikin halin rashin tsaro ba.”

Ya ƙara da cewa za a ƙarfafa jami’an tsaro ta hanyar ba su horo, kayan aiki, alawus da makamai na zamani.

Sai dai tun daga lokacin, hare-haren ƴan ta’adda da ƴan bindiga sun ƙaru musamman a yankunan karkara inda aka kashe dubban mutane, wasu kuma suka shiga hannun masu garkuwa da mutane.

Misalai sun haɗa da kisan sojoji 36 a jihar Neja cikin watan Agustan 2023, da sace ɗalibai 137 a Kaduna cikin watan Maris 2024, da harin bam a Gwoza wanda ya hallaka mutane 32 cikin watan Yuni.

Haka zalika, rahotanni sun nuna cewa fiye da mutane 10,000 ne aka kashe a hare-haren da ƴan bindiga da ‘yan ta’adda suka kai tun bayan da Tinubu ya hau mulki, kamar yadda Amnesty International ta bayyana, ko da yake gwamnatin Najeriya ta ƙi amincewa da wannan ƙididdiga ba tare da ta fitar da ta ta ba.

Bisa bayanan ACLED, mutane 7,472 ne suka mutu yayin da aka yi garkuwa da mutane 12,584 daga Mayu 2023 zuwa Mayu 2025.

A cewar mai ba da shawara kan harkokin tsaro na ƙasa, Nuhu Ribadu, “Fiye da ƴan ta’adda 13,000 aka kashe a yankin Arewa maso Gabas, yayin da wasu 124,408 suka miƙa wuya tare da iyalansu.”

Ribadu ya ce, “A ƙoƙarin da muke yi ta hanyar sasanci, wasu fitattun shugabannin ƴan bindiga fiye da 35 sun ajiye makamansu, musamman a ƙarƙashin shirin ‘Kaduna Model’.”

KARANTA WANNAN MA: TASHIN BAMA-BAMAI: Ƴan Boko Haram Sun Hallaka Fasinjoji 9 A Borno

A yayin da wasu jihohi kamar Kaduna da Katsina suka fara samun raguwar hare-hare, jihohin Zamfara, Sokoto da Neja sun ci gaba da fama da matsalar inda maharan ke dawo da hare-haren bayan yarjejeniyar sulhu ta gagara aiki.

A ɓangaren Arewa maso Gabas, ƙungiyar Boko Haram da ISWAP sun ƙara kai farmaki ga fararen hula da jami’an tsaro, yayin da sabbin ƙungiyoyi masu tasowa irin su Mahmuda da Lakurawa suka bayyana a Sokoto da yankin da ke kusa da gandun dajin Kainji.

Kamar yadda bayanai suka nuna, Arewa maso Yamma ta fi yawan asarar rayuka da samun garkuwa da mutane inda mutum 2,456 suka mutu, aka kuma sace mutum 7,260.

A Arewa ta Tsakiya, mutum 2,291 aka kashe, aka kuma sace 2,674, yayin da a Arewa maso Gabas mutum 1,457 aka kashe, aka kuma sace mutum 944.

A Kudu, matsalolin garkuwa da mutane, rikicin ƙabilanci, ƴan ta’adda da masu fafutukar ɓallewa sun hallaka mutane da dama: Kudu maso Gabas mutum 536 aka kashe, Kudu maso Kudu mutum 458, yayin da aka sace 811 a yankin.

Duk da nasarorin da gwamnatin Tinubu ke iƙirarin samu, sauye-sauyen ɗabi’a, sauyin fasalin ƴan ta’adda da ƙarfafa sabon tsarin yaƙi da ta’addanci na buƙatar tsauraran matakai da ingantattun dabaru.

Tun bayan da Tinubu ya ke kira ga hafsoshin tsaro da su kawo ƙarshen kisan jama’a, hare-haren sun ci gaba da ƙaruwa da sauyawa fasali, lamarin da ke bayyana cewa barazanar tsaro ba abu ne da za a warware cikin sauƙi ba, sai da cikakken tsarin aiki da haɗin kan al’umma.