
Shahararren masanin tattalin arziƙi kuma dan gwagwarmaya, Farfesa Pat Utomi, ya ƙaddamar da gwamnatin bayan fage ‘Big Tent Coalition Shadow Government’ don ƙalubalantar gwamnati mai ci da kuma bayar da shawarwari a matsayin kishin ƙasa, kamar yadda jaridar The PUNCH ta ruwaito.
Wannan gwamnati da ake kira da shadow government, da aka ƙaddamar da ita ta hanyar taron bidiyo a daren Litinin, zata dinga nazarin manufofin gwamnatin Tinubu da bayar da hanyoyin da za su inganta rayuwar ƴan Najeriya.
Sai dai, Ministan Yaɗa Labari da Wayar da Kan Jama’a na Ƙasa, Mohammed Idris, ya bayyana wannan mataki a matsayin kuskure cikin tsarin gwamnati da doka ba ta yarda da shi ba, yana mai cewa: “Najeriya ba ta bin tsarin majalisar dokoki kamar na Birtaniya, don haka babu sarari ga irin wannan dabara a tsarin mulkinmu.”
WANI LABARIN: Rashin Cin Jarabawar JAMB Alama Ce Ta Yaƙi Da Satar Jarabawa Na Nasara – Ministan Ilimi
Utomi ya dage cewa “matsalolin sauyin sheƙar ƴan jam’iyyu zuwa APC da tashe-tashen hankula a Benue da Plateau na nuna rashin aikin gwamnati yanda ya kamat,” yana mai cewa idan ƴan adawa ba su faɗi gaskiya ba, to suna taimakawa wajen wulaƙanta zaɓin jama’a.
Ya ce: “Muna cikin yanayi mai cike da ƙunci inda mutane suka daina fatan alheri, saboda haka dole ne mu motsa su daga wannan dogon bacci na rashin fatan canji.”
Ya bayyana sunayen mambobin majalisar gwamnatin bayan fagen da suka haɗa da Oghene Momoh, Cheta Nwanze, da Dele Farotimi a matsayin shugaban hukumar kula da shugabanci nagari.
Farfesan ya ƙara da cewa gwamnatin bayan fagen zata dinga gudanar da zaman majalisa duk sati don nazarin manufofi da bayar da shawarwari kan ilimi, kiwon lafiya, tsaro, da gyaran kundin tsarin mulki, tare da shan alwashin yaƙar talauci da karya tsarin da ya hana tattalin arziƙi bunƙasa.