
Daga: Mika’il Tsoho, Dutse
Gwamnatin Jihar Jigawa ta gudanar da bikin makon shayar da jarirai da nonon uwa na duniya, inda Uwargidan Gwamnan Jihar, Hajiya Khadija Umar Namadi, ta roƙi maza su mara wa matan da ke shayarwa baya domin cimma shayar da jariri da nono zalla na watanni shida.
A wurin taron da aka gudanar a cibiyar kiwon lafiya ta Kachi, Uwargidan ta hannun matar mataimakin gwamna, Hajiya Aisha Aminu Usman, ta yi kira ga gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu su samar da ɗakunan shayarwa a wuraren aiki.
“Shayarwa ba kawai bayar da abinci ba ne, rayuwa ce, kariya ce, da nuna ƙauna,” in ji ta, tana bayyana ta a matsayin “rigakafin farko” na jariri da ke magance matsalar rashin abinci mai gina jiki, cututtukan yara da na uwa.
Ta yi gargaɗin cewa mata da dama, ciki har da ma’aikata da ƴan kasuwa, na fuskantar zaɓin ko dai su ci gaba da aiki ko kuma su kula da jariransu, tana mai cewa: “Wannan bai kamata ba.”
- JIGAWA: Garko Ta Haɗejia Na Cikin Damuwa, Ɗaruruwan Almajirai Da Iyalai Sun Rasa Matsugunnai Sakamakon Mamakon Ruwan Sama
- KATSINA: Aƙalla Mutane 50 Ne Suka Mutu a Hare-Haren Malumfashi
- BORNO: Ƴan Boko Haram Sun Kashe Jami’an Tsaro Sun Yi Garkuwa Da Wasu A Konduga
- Sanata Wadada Ya Bayyana Ficewa Daga SDP Saboda Rikicin Da Ya Ƙi Ci Ya Ƙi Cinyewa
- TATTALIN ARZIƘI: Ajiyar Kuɗin Waje ‘Foreign Reserve’ Na Najeriya Ya Kai Dala Biliyan 41 – Fadar Shugaban Ƙasa
Uwargidan ta jaddada cewa “samar da ɗakin shayarwa bai kamata a ɗauke shi a matsayin gata ba, sai dai a matsayin fifikon manufofi,” tare da kiran shugabanni su ɗauki hakan a matsayin zuba jari a “makoma mai inganci da lafiya.”
Ta bayyana cewa duk cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko a ƙarƙashin Gwamna Malam Umar Namadi an daidaita su don tallafa wa mata masu shayarwa, tare da horas da masu aikin sa kai a ƙauyuka don wayar da kan al’umma kan abincin jarirai.
“Shayarwa ba aikin iya uwa kaɗai ba ne, aikin al’umma ne,” in ji ta.
Jami’in kula da Ingancin Abinci na Jihar Jigawa, Muhammad Abdullahi, ya bayyana shayar da jariri nonon uwa zalla a matsayin “hanya mafi inganci da araha wajen ciyar da jariri,” amma ya nuna damuwar cewa, kashi 29–30% ne kawai daga cikin mata a Jigawa ke yin hakan bisa ga rahoton NDHS na 2023.
Ya yi kira ga iyaye maza, sarakunan gargajiya, da shugabannin addini su tallafa wajen wayar da kan jama’a kan amfanin shayarwa ga ci gaban lafiyar yara a jiki da ƙwaƙwalwa.