A yayin da matsin tattalin arziƙi ke ƙara tsananta ga talakawan Najeriya, Jaridar NIGERIAN TRACKER ta gano cewar a Jami’ar Bayero da ke Kano, iya ɗalibai 5,000 ne suka yi rijistar komawa jami’ar cikin ɗalibai 30,000 da suka kammala hutu.
Jaridar ta gano cewar, jami’ar ta sanya ranar 21 ga watan Yulin nan a matsayin ranar rufe rijistar ɗalibai masu komawar domin fara sabuwar shekarar karatu.
Kuɗin yin rijistar yin karatu a Jami’ar Bayero dai, na tsakanin naira dubu 94 zuwa kusan naira dubu 170, gwargwadon darasin da ɗalibi ke ɗauka.
Ko da a shekarar karatun da ta gabata, gwamnatin Jihar Kano ƙarƙashin Abba Kabir Yusuf ta biya wa ƴan asalin Jihar Kano da ke karatu a jami’ar kuɗin rijistar.
To sai dai kuma, a halin da ake ciki yanzu, shugaban ƙungiyar shugabannin ajuzuwa na jami’ar, Ali Redah, ya rubutawa jami’ar buƙatar ƙara wa’adin dakatar da rijistar ko kuma a bayar da damar biyan wani ɓangare na kuɗin.