Wani tsohon ma’aikacin Hukumar Ilimi Matakin Farko ta Jihar Adamawa mai suna Aminu Mahdi ya faɗa komar ƴansanda bayan an zarge shi da kashe matarsa ta hanyar duka.
Dattijo Aminu, ɗan shekara 63 a duniya, wanda ya fito daga Mazaɓar Yelwa a Ƙaramar Hukumar Mubi ta Arewa, ya haiƙewa matarsa ta biyu Hadiza Zubuchi ƴar shekara 46, saboda ta hana shi ya kwanta da ita.
Wanda ake zargin, wanda ya amsa laifinsa, ya faɗa wa ƴansanda cewar, bai yi nufin matarsa ta mutu ba, kamar yanda Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar Ƴansandan Jihar Adamawa, SP Suleiman Nguroje ya bayyana.
KARANTA WANNAN: Wani Mutum Ɗan Shekara 50 Ya Kashe Agolan Gidansa A Jigawa
A wata tattaunawa da Nguroje yai da manema labarai a jiya Alhamis ya ce, Aminu ya koma gida da misalin ƙarfe 9 na dare a ranar Lahadin da ta wuce, 27 ga Agusta, 2023 inda ya tarar da yanayin da kai shi ga kawo ƙarshen rayuwar matarsa.
Nguroje ya ce, bayan Aminu ya ci abinci ne, ya canja kayan jikinsa, sai ya tafi ɗakin matarsa domin kwana a can, amma sai matar ta sa ta hana shi kwanciya a gadonta.
Da matar ta hana shi taɓa jikinta ta kuma matsa a kan hakan, sai kawai yai ta dukanta da sanda, dukan da yai yawa a kan matar ta sa wadda ya aura a shekarar 2016, sai yai sanadiyyar mutuwarta nan take.
Cikin da-na-sani, da ya ke faɗawa ƴansanda yanda lamarin ya faru, Aminu ya ce, “Ban yi tsammanin cewar abin da ya faru zai faru ba. Kuskure aka samu.”