Gwamnan Jihar Delta, Sheriff Oborevwori ya amince da a ɗebi malaman firamare, ƙananan ma’aikatan ofis da masu gadi a ƙananan hukumomi 22 na jihar.
Shugaban Ƙungiyar Ƙananan Hukumomi ta Najeriya, ALGON reshen Jihar Delta, Victor Ebonka ne ya bayyana hakan lokacin da yake ganawa da manema labarai a ƙarshen zaman tattaunawar da a kai kan Asusun Haɗaka na Jiha, JAAC a jiya Juma’a.
Labari Mai Alaƙa: Ɗan Majalissar Jigawa Mai Wakiltar Birnin Kudu Zai Nemawa Matasa Guraben Karatu
Ebonka ya ce, an bayar da umarnin ne a wajen zaman JAAC, yayinda amincewar ke nufin za a ɗebi ma’aikatan ne gwargwadon buƙatar kowacce ƙaramar hukuma.
Kowacce ƙaramar hukuma cikin ƙananan hukumomin 22 cikin 25 na jihar, zata ɗebi ma’aikatan ne gwargwadon adadin waɗanda suka yi ritaya ko mutu a ƙaramar hukumar.
Shugaban na ALGON ya kuma musa raɗe-raɗin da ake yi na cewar kuɗaɗen da ƙananan hukumomin suke samu ya ragu, inda ya ce kudin da suka samu a watan Yulin nan irin wanda suka saba samu ne.
