Wasu ƴanmata guda uku sun mutu a sanadiyyar nutsewa a ruwa da misalin ƙarfe 11 na ranar Asabar a wani gulbi da ke yankin Ƙaramar Hukumar Buji a Jihar Jigawa.
Ƴanmata sun faɗa wannan hatsarin ne lokacin da suke yin ciyawa domin kaiwa dabbobinsu a gida.
Maimagana da yawun rundunar Civil Defence ta Jihar Jigawa, ASC Badaruddeen Tijuana wanda ya tabbatar da faruwar hatsarin a wata sanarwa da ya saki jiya Lahadi a Dutse, ya bayyana cewa waɗanda hatsarin ya rutsa da su sun haɗa da Fatima Sule ƴar shekara 12 da Nasiya Sale ƴar shekara 12 da kuma Huwaila Sa’adu ƴar shekara 13 dukkansu ƴan ƙauyen Tulla da ke Ƙaramar Hukumar Buji.
Badaruddeen ya ƙara da cewar, jami’an Civil Defence sun garzaya ƙauyen, bayan sun samu kira daga mutanen ƙauyen da misalin ƙarfe 11:10 na safe domin zuwa ceton rayukan ƴanmatan.
To sai dai bayan ɗebe kimanin mintuna 30 ana bincike, jami’an sun samu nasarar gano gawarwakin ƴanmatan ne ba tare da sun same su da rai ba.
An kuma garzaya da gawarwakin ƴanmatan zuwa cibiyar lafiya da ke kusa da ƙauyen, inda jami’an lafiya suka tabbatar da mutuwarsu.
Bayan haka ne aka miƙa gawarwakin ga iyalan mamatan waɗanda suka gudanar musu da jana’iza kamar yanda addinin Musulunci ya tanada.