Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Wasu Da Ake Zargin Makiyaya Ne Sun Kai Hari Wata Makaranta, Sun Kashe Ango Da Amarya

Wani ango da amaryarsa, sabbin aure, sun rasa ransu a yayin da wasu da ake zargin makiyaya ne suka kai hari kan Makarantar Sikandire ta BECO Comprehensive da ke garin Kwi a Ƙaramar Hukumar Riyom ta Jihar Plateau.

Lamarin dai ya faru ne a ranar Litinin a makarantar da ma’auratan ke koyarwa waɗanda suka yi aure a watan Maris, yayin da a lokacin harin kuma mataimakin shugaban makarantar ya tsira da raunukan harbin bindiga.

Da yake bayani kan abun da ya faru, shugaban makarantar, Dandoro Gyang ya bayyana cewar, a lokacin da aka kai harin, malaman makarantar na zaman tattaunawa a harabar makarantar lokacin da waɗanda ake zargin makiyaya ne tafe da shanunsu suka kai musu harin ta hanyar yin harbin kan-mai-uwa-da-wabi.

KARANTA WANNAN:

Ya ƙara da cewar harbe-harben ne suka sa malaman suka tarwatse suka nemi wajen tsira, a daidai lokacin da ɗaya daga cikinsu ya rasa ransa, sai kuma ɗayar ta mutu a asibiti, yayin da mataimakin shugaban makarantar, Dalyop Emmanuel Ibrahim ya tsira da raunuka.

Wannan harin dai ya jawo Shugaban Ƙungiyar Berom Youth Moulders, Solomon Dalyop yin kira ga gwamnatin Jihar Plateau da ta haramta yawon kiwo a jihar.

Ya ce, wannan kiran ya zama dole ne, saboda ana fakewa da kiwon wajen tayar da hankalin jama’a da cutar da dukiyoyinsu da rayukansu.