Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Wasu Fitattun Mutane Sun Zama Shugabannin Ƙungiyar One Voice Development Initiative

Ƙungiyar One Voice Development Initiative ke da muradin inganta shugabanci na gari, nuna gaskiya a harkokin jama’a, da ci gaban siyasa, ta sanar da sabbin shugabanninta na ƙasa.

Abbas Abdullahi, CISSP, IPMA, ne ya zama shugaban ƙungiyar na ƙasa, inda zai jagoranci ƙungiyar wajen kare ƙa’idojin dimokaradiyya da bunƙasa tsare-tsare masu kyau.

Kwamared Sani Garba, ƙwararren masani a fannin sadarwa da gudanar da ofis, zai riƙe mukamin Daraktan Sadarwa da Tsare-Tsare na ƙungiyar, kuma zai kula da sakatariyar ƙungiyar.

Ita Khadija Muhd, mai goyon bayan samar da adalci tsakanin jinsi da ƙarfafar mata, ta zama Daraktar Harkokin Mata, inda za ta mayar da hankali wajen inganta tsare-tsaren da suka shafi damawa da kowa a al’amura.

Sai Ali Maiwada, wanda ƙwararren masani ne a fannin tsare-tsare da manufofin siyasa, zai jagoranci sashen bincike da tsare-tsaren manufofin ƙungiyar a matsayin Daraktan Tsare-Tsare da Yaɗa Manufa.

Shi kuma Nura Saghir Muhd, ƙwararren masani a fannin dabarun siyasa, an naɗa shi a matsayin Daraktan Siyasa da Harkokin Jam’iyyu don ƙarfafa haɗin kai da jam’iyyun siyasa da sauran masu ruwa da tsaki.

Mal. Abubakar AbdulKadir Dangambo, ƙwararren masani ne a fannin yaɗa labarai da hulɗa da jama’a, shine zai riƙe mukamin Daraktan Yaɗa Labarai domin ƙara faɗaɗa tasirin ƙungiyar a cikin jama’a.

Ita ma Haj. Hindatu Bashir, sananniyar mai ƙarfafa gwiwar al’umma, ta zama Daraktar Tuntuɓar Jama’a don samar da goyon baya ga shirye-shiryen ƙungiyar daga ƙasa.

Sauran shugabannin sune Hajiya Hauwa Muhd a matsayin Daraktar Kuɗi da Samar da Walwala, Kwamared Auwal Ali a matsayin Daraktan Hulɗa da Jama’a da Ƙungiyoyi, da kuma Alhaji Lawal Muhammad Riba a matsayin Shugaban Kwamitin Amintattun ƙungiyar.

A cewar Daraktan Harkokin Yaɗa Labarai na ƙungiyar, Abubakar Dangambo, waɗanda aka naɗa ɗin zasu yi aiki tukuru wajen ƙarfafar shugabanci na gari, tabbatar da gaskiya a harkokin jama’a, da haɓaka cigaban siyasa, tare da tabbatar da cewa muryoyin jama’a na da muhimmanci da kuma tasiri.