Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Wasu Gwamnonin Na Shirin Komawa APC Kuma Zargin Ƙuntatawa Ba Gaskiya Ba Ne – Gwamnan Nasarawa

Gwamnan Jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya bayyana cewa jam’iyyar APC na ƙara samun manyan ƴan siyasa daga jam’iyyun adawa da ke sauya sheƙa zuwa gare ta, yana mai musanta zargin ƙuntatawa da tsoratarwa daga ɓangaren gwamnati.

A hirar sa da Channels Television, gwamnan ya ce jam’iyyar na nazari da yin shiri domin tinkarar zaɓen 2027, musamman bayan da wasu shugabannin jam’iyyun adawa suka haɗu domin kafa babbar haɗaka.

“Mu ma muna shiri, kamar yadda su ke shiri, domin wannan siyasa ce. A ƙarshe, wanda ya fi shiryawa shi ne zai yi nasara,” in ji gwamnan.

WANI LABARIN: Ana Ayyukan Raya Ƙasa Ne A Inda Zasu Yi Amfani, Martanin Abdulaziz Abdulaziz Ga Kwankwaso

Ya ƙara da cewa: “Kullum ana samun sabbin gwamnoni da sanatoci da ke komawa APC. Wannan shiri ne, kuma ba sihiri ba ne.”

Wannan furuci na zuwa ne kwana ƙalilan bayan taron ƙungiyar jam’iyyun adawa da ya gudana a cibiyar Yar’Adua a Abuja, inda aka bayyana ADC a matsayin sabon dandali da zai ɗauki nauyin fafatawa da APC a 2027.

Gwamnan ya musanta zargin cewa wasu ƴan siyasa na jin tsoron shiga wannan haɗaka saboda tsangwama daga gwamnati, yana mai cewa jam’iyyar APC ta fi ƙarfin yin haka.